Kotun Ƙoli ta jaddada amincewa da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta zartas kan tsohon babban jami’in Hukumar Fenshon ‘Yan Sanda John Yusuf Yakubu, wanda kotun ta ɗaure shekaru 6 da kuma tarar amayar da naira biliyan 22.9 da ya sata.
EFCC ce ta ɗaukaka ƙara bayan Mai Shari’a Abubakar Talba na Babbar Kotun Abuja ya kama John Yakubu da satar Naira biliyan 24, amma kuma ya ɗaure shi shekaru 2 a gidan kurkuku, ko kuma ya biya tarar Naira 750,000 kacal.
‘Yan Najeriya sun cika da mamakin wannan irin makauniyar shari’a. Ƙarin abin haushi kuma, sai John Yakubu ya zaro kuɗi a cikin motar sa ya biya tarar Naira 750,000 nan take.
Hukuncin ya tayar wa EFCC hankali, daga nan ta ɗaukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda Babban Mai Shari’a Emmanual Agim ya sake hukuncin zuwa ɗaurin shekaru 6 da tarar naira biliyan 22.9 a cikin watan Maris, 2018.
John Yakubu ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli, inda a yau Laraba ya jaddada ɗaurin shekaru shida kan John Yakubu da kuma tarar naira biliyan 22.9, wadda aka ce haƙƙin ‘yan fenshon ɗan sanda ce, sai ya biya.
Alkalai 5 ne na Kotun Ƙoli duk suka amince da hukuncin, wanda Babban Mai Shari’a Tijjani Abubakar ya karanto hukuncin.
Sauran Manyan Alƙalan sun haɗa da Helen Ogunwumiju, Musa Dattijo, Muhammad Nwere da Adamu Jauro.
Sun la’anci hukuncin farko da Mai Shari’a Abubakar Talba ya yi. Sun ce hukuncin cin fuska ne ga fannin shari’a.
Idan ba a manta ba, Hukumar Kula da Alƙalai ta Kasa (NJC) sai da ta dakatar da Abubakar Talba tsawon shekara ɗaya, saboda hukuncin tarar Naira 750,000 da ya yanke wa ɓarawon naira biliyan 24.
Daga baya Talba ya shiga ya fita, ya koma aikin sa, har aka ƙara masa muƙami zuwa Kotun Ƙoli.