Sanatan dake wakiltar gundumar yankin da ya kunshi mahaifar shugaban Kasa, karamar hukumar Daura, Sanata Ahmed Babba-Kaita ya fice daga APC zuwa PDP.
Babba-Kaita ya canja sheka zuwa PDP ne ranar Laraba, saboda rashin jituwa da suke samu tsakanin sa da gwamnan jihar Aminu Masari.
A wasikar da ya aika wa PREMIUM TIMES, kakakin sanatan Abdulkadir Lawal, ya ce sanata Babba-Kaita ba dan amshin shata bane.
” Na ba irin ‘yan siyasan nan bane da ake yi wa lakani da ‘yan amshin shata. Ba zan amince da haka kuma hakan shine dalilin da ya sa na tattara kaya na na fice daga APC.
” Jam’iyyar PDP ce jam’iyyar da ta dace da ni ba APC ba. Saboda haka na hakura da APC na koma gidan da ya fi dacewa da ni a siyasance. ”
Sanata Babba-Kaita ba su ga maciji da gwamnan jihar Katsina Aminu Masari wanda ya ke zargi da yin babakere a jam’iyyar APC a Katsina ba tare da ya baiwa sauran yan jam’iyyar dama su taka rawar su a ba domin cigaban jam’iyyar.