Mataimakin bulaliyar marasa rinjaye a majalisar Dattawa, sanata Ibrahim Ɗanbaba ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP.
Ɗanbaba ya shaida wa majalisa cewa rikicin da ya ƙudundune jam’iyyar PDP da yaƙi ci yaƙi cinyewa shine ya sa ya hakura da jam’iyyar ya koma jam’iyyar APC.
Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan ne ya karanta wasikar sauya sheka da Sanata Danbaba yayi a zauren majalisar.
” Jam’iyyar PDP ta rufta cikin gagarimar ruɗani. A kullun sai kaji wani wurin da aka ɗinke ya sake barkewa. Hakan ya sa ba zan iya cigaba da zama a cikin jam’iyyar ba.
” Babbar matsalar ma ta fi muni a yankunan jihohi. Wannan yasa ina ji ina gani dole gashi na hakura da jam’iyyar saboda ba zan iya zama a cukuikuye wuri ɗaya ba sannan ba kullum ana cikin ruɗani
” Bayan nazari da nayi na gano APC ce jam’iyyar da tafi dacewa dani da manufofi na ba PDP ba da nake a ciki tuntuni.
Saidai kuma wasu jigajigan PDP a zauren majalisa sun nemi a dakatar da Ɗanbaba daga canja shekar amma hakan bai yiwu ba.
Shugaban majalisar ya ce dalilan da Ɗanbaba ya bayyana masu karfi ne kyma yana da ikon canja sheka idan har abu yi muno kamar yadda aya bayyana a kowace jam’iyyar ya ke.