Rundunar Ƴan sandan jihar Kano ta sanar da hana yin tashe a azumin bana.
Tashe al’ada ce ta wacce ake yi a kasar Hausa daga 10 ga watan Ramadan.
Yara har da manya kan riƙa bi suna wake ana basu taro, sisi.
A wannan shekara, rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta hana ‘Tashe’ ne saboda kauce wa baragurbin mutane, wato batagari kada su saje cikin masu tashe suna aikata munanan ayyuka.
A cikin sanarwar Kwamishinan ƴan sandan jihar Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi ya gargaɗi iyaye su ja wa ƴaƴan kunne kada su kuskura su karya wannan doka.
Discussion about this post