Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra, ya bayyana cewa ya tsamo kwamishinonin sa 20 daga cikin mutum 22,000 da suka nemi muƙaman.
Ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke rantsar da sabbin kwamishinonin a Fadar Gwamnatin da ke Awka, babban birnin jihar Anambra.
Ya hore su da su tabbatar da sun yi aiki tuƙuru a cikin gaskiya, ƙwarewa da kuma kishin jiha.
Soludo ya ce gwamnatin sa za ta kafa dokar-ta-ɓaci a dukkan ɓangarorin ayyuka, amma daga harkar tsaro ce zai fara kafa wa dokar-ta-ɓaci ɗin.
“Dukkan ɓangarorin ma’aikatun gwamnati za a ba su kulawar da ta cancanta kuma ta wajibta a ba su. Za mu fara daga fannin tsaro, wanda tun bayan hawan mu mulki muka fara yin wani yunƙuri.” Inji Soludo.
Sannan kuma ya ce amma ya kauce wa tsarin da baya aka sani wajen naɗa kwamishinoni da ma’aikatun da ana tura kowane sabon kwamishina.
A ya ce shi a yanzu ya zaɓi kwsmishinoni ne a bisa cancanta da ƙwarewar sa a fannin ilmin da ya fi naƙalta.
“Fiye da mutum 22,000 suka rubuta wasiƙun neman kujerun muƙamai daban-daban. Sama da 1,000 suka nemi zama kwamishina.
“To daga wannan jerin sunayen ne na zaƙulo kwamishinonin nan 20 da kuma wani guda ɗaya da Majalisar Dokoki ba ta tantance shi ba tukunna. Saboda na miƙa wa Majalisa sunan sa daga baya.” Haka Soludo ya shaida wa ɗimbin mahalarta bikin rantsar da kwamishinonin.
Ya ce kowane kwamishina za a ba shi taken sa ‘Anambra Vision 2070, wanda daftari ne da kwamitin miƙa mulki ga gwamnatin sa ta ƙirƙiro kafin a damƙa masa mulki.
Ya ce daftarin ya shafi sama da mutum miliyan 15 ‘yan asalin Anambra.