Gwamnatin jihar Bauchi ta saka dokar hana walwala a garin Gudun Hausawa dake kusa da garin Bauchi.
Hakan ya biyo bayan rikicin kabilanci ne da ya ɓarke tsakanin mazauna garin ranar Laraba.
Wannan sanarwa na kunshe a takarda da mashawarcin gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai Mukhtar Gidado ya raba wa manema labarai a garin Bauchi.
Gidado ya ce sanadiyyar rikicin mutum uku sun mutu, mutane da dama sun ji rauni sannan an kona gidaje da dama a garin.
Ya ce jami’an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu a tada rikicin.
“Gwamnan jihar Bala Mohammed ya sa a gina ofishin ‘yan sanda a wannan yanki sannan an kuma aika da jami’an tsaro da za su rika sintiri domin tabbatar da zaman lafiya tare da gudanar da bincike domin gano sanadiyyar ɓarkewar rikicin.
Gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane a wannan gari da jihar baki daya ba.
Discussion about this post