Sakamakon binciken da ‘Nigeria Security Tracker (NST)’ ta gudanar ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Maris an yi garkuwa da mutum 1,484 sannan an kashe mutum 2,968 a Najeriya.
Wannan sakamakon rahoto ne da ake bugawa duk mako daga wasu jaridun kasashen waje masu bin diddigi akan abubuwan dake faruwa a Najeriya.
Yawan mutanen da suka mutu a Najeriya
Sakamakon binciken ya nuna cewa an fi kashe mutane a yankin Arewa maso Yammacin kasar fiye da kowace bangare a kasar. Akalla mutum 1,103 ne aka kashe a wannan yanki.
Na biye da haka itace yankin Arewa ta Tsakiya inda aka kashe mutum 984 sannan mutum 488 a yankin Arewa maso Gabas.
An kashe mutum 181 a yankin Kudu maso Gabas, mutum 127 a Kudu maso Yamma sannan mutum 85 a Kudu maso Kudu.
Tun a shekaran 2017 ne ‘yan bindiga ke kai wa mutane hari tare da kisan mutane a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
‘Yan bindigan kan Kai wa mazauna karkara hari su cinna wa gonaki wuta.
A yankin Arewa maso Gabashin kasar nan Boko Haram sun kashe mutum sama da 35,000 sannan mutum sama da miliyan 3 sun rasa gidajen su a dalilin hareharen ƴan bindiga da ƴan ta’adda.
A yankin Kudu maso Gabas ‘yan kungiyar kabilan Inyamurai na IPOB da ESN sun kashe mutane da dama a yankin.
Wadannan mahara na kai wa gine-ginen gwamnati hari, suna Kuma kashe jami’an tsaro sannan suna yin garkuwa da mutane tare da karban kudin fansa.
An kashe mutum 998 a watan Janairu, mutum 756 a Fabrairu sannan mutum 1,214 a Maris.
Yankin Arewa
Sakamakon binciken ya nuna cewa yankin Arewa ta fi samun yawan mutanen da aka kashe a kasar nan.
A Arewa an kashe mutum 2,575 wato Kashi 86.8% amma a yankin Kudu an kashe mutum 393 wato kashi 13.2%.
A yankin Arewa jihohin da suka yi kaurin suna a kisan mutane sun hada da jihar Neja inda aka kashe mutum 840, Zamfara-404, Borno- 392, Kaduna 332 da Kebbi 114.
Garkuwa da mutane
Sakamakon binciken ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane sau 746 a Arewa maso Yammacin kasar nan.
A Arewa ta Tsakiya an yi garkuwa da mutane sau 547 sannan an yi garkuwa da mutane sau 62 a Arewa maso Gabashin kasan.
An yi garkuwa da mutum 53 a Kudu maso Gabas, mutum 44 a Kudu maso Kudu da mutum 36 a Kudu maso Gabas.
Mutum 1,354 ne ke zama a Arewa inda daga cikin su ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kashi 91.2% sannan a yankin Kudu da ake da mutum 130 an yi garkuwa da kashe 8.8% daga cikin su.
An Yi garkuwa da mutum 623 a Janairu, mutum 342 a Fabrairu sannan mutum 519 a Maris.
Jihohin Niger 458, Kaduna 448, Zamfara 138, Katsina 138, Katsina 106 da Kogi 51 na cikin jihohin da suka yi kaurin suna a yawan yin garkuwa da mutane a Najeriya.
Discussion about this post