Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa hukumomin sojan Najeriya, SSS da ‘yan sanda na take haƙƙin jama’a a ƙasar saboda lalacewar rashawa da sakwarkwacewar sashen shari’a.
Gwamnatin Amurka ta bayyana haka a cikin wani Rahoton Take Haƙƙin Jama’a na 2021 da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta wallafa, kuma ta fitar a ranar Talata.
Rahoton ta taɓo batutuwa da dama, ciki har da take haƙƙin jama’a, rashawa, cin hanci da satar kuɗin gwamnati da kuma yadda ɓangarorin hukumomin soja, SSS da na ‘yan sanda ke yawan take haƙƙin jama’a ba gaira ba dalili.
Sannan kuma Amurka ta zargi jami’an tsaron Najeriya su na aikin da ya saɓa ƙa’idar dokar farar hula, ba tare da jin tsoron za a hukunta su ba, ko tunanin mummunar illar da ɓarnar da suke tabkawa za ta haifar ba.
“Cin zarafi da cin zalin, rashawa da cin hanci da satar kuɗin gwamnati, sun kasance manya a sahun gaban matsalolin da ke addabar ɓangarorin sojojin Najeriya, SSS da ‘yan sanda.” Haka dai Gwamnatin Amurka ta bayyana.
“Duk da cewa ‘yan sanda, sojoji da SSS su na a ƙarƙashin mulkin farar hula ne, amma su kan wuce-gona-da-iri su na take haƙƙin jama’a.
“Ko dai su riƙa yin amfani da ƙarfin tsiya su na dannewa da tarwatsa masu zanga-zanga, ko wajen kamen masu laifi, ko kuma amfani da barkonon tsohuwa, daga nan kuma su riƙa bin masu zanga-zanga su na lakaɗa masu dukan tsiya.
Wani rahoto da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai lura da Laifukan Ƙwayoyi (UNODC), ya fallasa cewa ‘yan Najeriya da jamian karɓar haraji na ƙasar ne suka fi karɓar cin hanci da toshiyar baki.
Rahoton ya ce kashi kashi 29.7 na cin hanci da toshiyar bakin naira biliyan 400, duk ‘yan sanda a ke ba kuɗin. Kuma sai ka biya sannan za yi maka abin da ka nema.
Rahoton ya kuma nuna yadda kwamitin sirri da hukumomin tsaro ke kafawa su binciki zarge-zargen cin zarafi ke kasancewa a cikin sirri, ba a jin yadda lamarin, sai a bar ‘yan Najeriya cikin duhu.
Amurka ta kafa hujja ko misali da Kwamitin Binciken Zargin Kashe-kashen #EndSARS na Jihar Legas, cikin 20220.
Ta kuma yi tsokaci kan yadda ake garƙame mutanen da ba su ji ba, ba su kuma gani ba.
Discussion about this post