Mazauna garin Mada dake karamar hukumar Gusau suna yin ƙaura daga garin a dalilin fargabar kawo musu hari da suke yi wanda suka ƴan bindiga za su iya yi a koda yaushe.
Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar haka tana mai cewa tuni ta aika jami’anta sukai wa mutane ɗauki sannan da tabbatar da zaman lafiya a garin na Mada.
Wani mazaunin garin Mada Yusuf Anka ya bayyanawa PREMIUM TIMES cewa harin ramuwar gayya ce ya kawo ƴan bindigan wanna gari.
” A kwanakin baya ƴan banga karkashin shugaban su Ɗanmudi Mada sun kai wa ƴan bindiga hari inda suka halaka wani gogarman su mai suna ‘Malaikan Hausawa’ wanda shi burinsa a kullum shine ya ga bayan duk wani bahaushe da ya yi gaba da gaba da shi.
Ɗanmudi ya kai farmaki sansanonin ƴan bindiga inda ya kashe mahara da dama ciki har da ‘Malaikan Hausawa’.
” Wannan shine dalilin da ya sa ƴan bindigan suka yo shiri ta musamman duka dira garin Mada. Sun yi arangama da ƴan banga na tsawon awowi, amma kuma daga karshe sai suka ci karfin ƴan bangan amma kuma kafin su kai ga shiga garin jami’an tsaro sun isa garin.
Amma fa mutanen garin sun ci gaba da kwashe kayan su suna yin ƙaura daga garin. ” Ba za mu iya cigaba da zama a garin ba domin akwai yiwuwar ƴan bindigan za su dawo tunda basu iya kaiwa ga shiga garin ba.
” Ƴan bindiga na kwafe da wannan gari ba tun yanzu ba, domin suna cewa wai muna sanar da ƴan banga bayanai a kan su. Domin ko a cikin makon jiya sai da suka kama wasu ƴan bindiga suka yi rugurugu da su. Suka kashe su