Allah Ya sake zagayo da mu wata shekara, kuma cikin wata na Tara a kalandar Musulunci addinin gaskiya, wanda Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi don ya zama hanyar tsira ga wadanda suka bi shi. Watan da Allah Ya saukar Alqur’ani mai girma, shi ne watan kasafi ga bayin Allah, kuma watan ibada, watan gafara da rahama, watan da aka cikin sa Allah Ya ke yin kasafi duk abin da zai faru a shekara, yayin da Zai umarci mala’kunSa su rubuta.
Tafiya ta yi nisa sosai a cikin azumin wannan shekara, domin ga shi har muna tunkarar goman karshe a cikin kwanakin wannan wata mai alfarma da daraja. Kwanakin da suka kasance tamkar gwalagwale a cikin duhun dare, domin a cikin su ne ake rubanya ibada ga Allah (S.W.T), shi Ma Ya rubanya ladan ibadar ninkin ba ninkin ga wanda ya aikata ta. Ma’ana, in mutum ya yi sadaka a cikin wadannan kwanaki to ladan ta ba dai dai yake da na sauran kwanaki ba ko wasu watanni da suka wuce a baya. To kamar haka ne ga duk wani aikin ibada da mutum ya gabata, kamar Sallah, zakkah da zikiri.
Kuma a cikin wadannan kwanaki ne Allah Ya saukar da wani dare mafi daraja daga cikin darare. Daren da darajar sa watanni dubu, wato fiye da shekara tamanin kenan (80yrs). Wannan dare shi Allah Ya kira…LAILATUL QLAILATUL QADR, wato daren kaddara. Daren da Allah Ya ke mika wa mala’iku (muwakkaluna) kundin aikin su na wata shekara domin aiwatar wa, kwatankwacin yadda shugabannin mu suke yi wajen kasafin kudi a wannan duniya.
A cikin wannan dare ne mala’iku ke sauka a saman duniya domin amsa bukatar bayin Allah masu ibada a cikin wannan dare, su dauke ta zuwa Allah. A cikin wannan dare ne Allah Ya ke yin gafara ga miliyoyin bayin Sa. A cikin sa yake amsa duk wata bukata tasu. A cikin sa Ya ke rahama da gafara. A cikin sa Ya ke rabon aljanna, kuma a cikin sa ne Ya ke rabon arziki. A cikin sa ne ni’ima take sauka ta lullube duniya tun daga yammaci har zuwa wayewar gari. A cikin wannan dare ake hana duk wata halitta da ba Dan Adam ba cutar da shi ta hanyoyi da dama, ko Dan Adam din ne ba a ba shi ikon cutar da dan uwansa, saboda rahamaniyya irin ta Ubangijin talikai.
A karshe ina yi mana addu’ar Allah Ya ba mu ikon dagewa da ibada a gareShi, a cikin RAMADAN da bayan ramadan. Ya ba mu kwarin gwiwar ci gaba da ayyukan ibada a cikin wannan wata. Ya ba mu ladan azumi cikakke. Ya sa mu dace mu rabauta da wannan dare na LAILATUL QADR. Ya sanya mu cikin bayin Sa da zai ‘yantar a cikin wannan wata. Ameen summa Ameen.
Muazu Muazu
Dan Jarida mai aiki da Freedom Radio, Kano.
08036433199
muazumj@gmail.com