Hukumar shirya gasar Firimiya ta Najeriya, LMC, ta ci tarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars naira miliyan 9.
Hukumar ta ce bayan haka za a kwashewa Pillars ɗin maki uku daga adadin makin da ta tara a kakar wasa ta bana.
Bayan haka kuma hukumar ta gargaɗi kungiyar Pillars cewa idan ta sake aikata laifi irin haka nan gaba, za a sake kwashe mata maki uku sannan a hukuntata.
Sauran hukuncin da aka yanke sun hada da, daga yanzu ƙungiyar zata rika buga wasannin ta na gida ne a filin wasa na MKO Abiola dake Abuja, bata ba Filin Sani Abacha dake Kano.
” An dakatar da filin wasa na Sani Abacha dake Ƙofar Mata daga ɗaukar dukkanin wasannin gasar NPFL har sai abinda hali ya yi.
” Sannan kuma Kano Pillars zata gyara motar kungiyar Katsina Utd da magoya bayanta suka lalata.