Jam’iyyar PDP mai adawa da APC ta yi kira ga hukumomin yaƙi da rashawa, wato EFCC da ICPC su binciki duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC wanda ya tsige naira miliyan 100 ya sayi fam ɗin takara.
PDP har yau ta ce abinci duk wanda ya fitar da naira miliyan 50 daga APC ya sayi fam, domin a tantance yadda aka yi suka samu kuɗaɗen.
Haka nan kuma ta ce ya dace idan dai har yaƙi da cin hanci da rashawa su gurfanar da duk wanda ya sayi fam ɗin a kotu, su caje shi da laifin damfara.
“Rashin hankali ne tantagaryar a ce za a sayar da fam ɗin takara naira miliyan 100 da kuma naira miliyan 50. Duk wanda ya tsige kuɗi ya saya, to ɗan damfara ne, a maka shi kotu kawai.” Inji PDP.
Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayi ne ya yi wannan kiran da kan sa, cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa Simon Imobo-Tswam ya sa wa hannu, kuma ya fitar a ranar Alhamis.
Kalaman na Ayu sun fito ne bayan da APC ta bayyana Naira miliyan 100 ce kuɗin fam na takarar shugaban ƙasa.
APC ta raba kuɗin gida biyu. Naira miliyan 30 kuɗin na-gani-ina-so, naira miliyan 70 kuma kuɗin fam. Kuɗi sun kama naira miliyan 100 kenan.
Shi kuma duk mai don fitowa takarar gwamna a zaɓen-fidda-gwani, zai biya Naira miliyan 50. Yayin da sanata zai biya Naira miliyan 20, ɗan takarar Majalisar Tarayya kuma zai biya Naira miliyan 10.
Yayin da masu takarar Majalisar Dokokin Jihohi za su biya naira miliyan 2 kowanen su.
Sai dai kuma APC ta amince ta yi wa kowane ɗan takarar da bai kai shekaru 40 ba, an yi masa ragin kashi 50 bisa 100 na kuɗin.
‘Baragurbin Munafukai’:
PDP ta ce makudan kuɗaɗen da APC ta yanka a biya na sayen fam ɗin takara ya fassara APC da cewa baragurbi ce, kuma munafika.
“Yanzu ‘yan Najeriya za su iya gani ƙuru-ƙuru cewa APC ba wata tsiya ba ce, sai gungun wasu ‘yan ta-kifen da su ka haɗa kai don kawai su karɓe mulki, su ƙaƙaba wa jama’a ƙuncin rayuwar babu gaira babu dalili. Ba su damu ba har ‘yan jam’iyyar su ma ƙaƙaba masu masifar tsadar rayuwa suke yi.”
Discussion about this post