Baya ga kasashen Korea Ta Kudu da Vietnam, Najeriya ce ƙasa ta uku a jerin kasashen da suka fi cin naman kare a duniya.
Wani mai gudanar da bincike Matthew Nash ya gano haka a bincike da ya gudanar na kasashen da suka fi sha’awar kiwon kare a shekarar 2022.
Sakamakon binciken ya nuna cewa baya ga cira tuta da Najeriya wajen cin naman kare Najeriya na cikin kasashen dake kashin baya wajen kafa dokokin kare hakkin karnuka da samar wa karnuka kiwon lafiya.
Kasashe da suka hada da Italy, New Zealand, Faransa, U.K da Jamus na daga cikin kasashen duniya da suka fi kula da karnuka ta hanyar samar musu da kiwon lafiya mai nagarta, saka dokokin kare hakkin karnuka da kiwon kare.
Duk da cewa tsarin dokokin Najeriya ta shekaran 1990 bangare na 495 ya nuna cewa ya kamata a rika kare hakin dabbobi wannan doka baya aiki a Najeriya.
Idan ba a manta ba a watan Yulin 2021 mutum kusan 18000 ne suka saka hannu a takarda domin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya hana cin naman kare a kasar nan amma shuru har yanzu.
Cin naman kare a Najeriya
A Najeriya jihohin Rivers, Cross Rivers, Filato da Kaduna na daga cikin jihohin da suka yi kaurin suna wajen cin naman kare.
Wadannan wurare sun fi sanin naman kare da sunan 404 sannan an fi cin naman a gidajen shan giya da Burkutu.
Discussion about this post