Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ƴan Najeriya na da mantuwa ne amma nasarorin da ya samu a harkar tsaro ya zarce waɗanda aka samu a lokacin mulkin Jonathan.
Buhari ya bayyana haka ne a jawabin sa a wurin taron APC da aka yi ranar Laraba a Abuja
” Idan ba a manta ba a lokacin da muka zo kan mulki, kananan hukumomi duka ke karkashin Boko Haram a jihar Barno, amma yanzu babu ko ɗaya da ke karkashin ikon su.
” Haka kuma a yankin Kudu Maso Kudu xan ma kowa ya san matsalolin da muka iske da kuma yadda myka kauda su.
” Yanzu a yankin Arewa Maso Yamma da Tsakiya ne ake samun matsalolin rashin tsaro, mutane na kashe junan su na babu gaira babu dalili. A nan ma zamu koya musu hankali nan bada dadewa wa ba.
Sai dai kuma ƴan Najeriya na ganin duk da nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu, a karkashin mulkinsa an fi fama da kashekashen mutane fiye da a lokacin gwamnatocin baya.
A yankin Arewa Maso Yamma da ya haɗa da jigar Katsina, jihar Shugaba Buhari, ƴan bindiga sun kashe mutane da dama sannan sun yi garkuwa da mutane mutane da dama da wasu har yanzu suna tsare a wurin su.
Jihohin Kaduna, Neja, Zamfara, Sokoto, Kebbi duk na fama da hare-haren ƴan bindiga babu ƙakkautawa.
Discussion about this post