Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya kori Sarakunan Zurmi da na Ɗansadau saboda samunsu da hannu dumu duma cikin harkallar ‘yan bindiga a jihar.
Sakataren yada labarai na mataimakin gwamnatin jihar Babangida Zurmi ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sanarwar hakan na kunshe ne a wata takarda da aka fitar bayan bincike da aka yi a jihar.
Kwamitin wanda Kwamishinan tsaron jihar Mamman Tsafe ya shugabanta ya ce an gayyaci sarakunan domin su kare kansu a wajen zaman kwamitin.
Sai dai kuma ba a bayyana duka abubuwan da rahoton kwamitin ya kunsa ba, baya ga bayyana wadannan sarakuna da irin taka rawar da suke yi wajen cigaba da hareharen da ke samu na ‘yan bindiga a jihar.
Idan ba a manta ba Alhaji Atiku Abubakar na Zurmi da Alhaji Hussain Umar Ɗansadau na daga cikin manyan sarakunan da gwamna Matawalle ya wanke da kyautar motocin alfarma a cikin farkon wannan wata.