A sakon taya kiristoci bikin Easter gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya yi kira ga mutane a jihar da su ci gaba da addu’o’i domin ganin an gama da Boko Haram da kuma yin maraba da tubabbun ‘yan Boko Haram.
Zulum ya fadi haka ne a wani takarda da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Isa Gusau ya fidda domin bukukuwa easter da aka yi daga jarshen makon jiya zuwa farkon wannan mako.
Ya ce Easter ya zo a daidai gwamnati na maraba da tubabbun’yan Boko Haram masu ɗinbin yawa
Zulum ya ce wannan shiri da gwamnati ta fara zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a jihar.
“A yakin da muke yi da Boko Haram sama da shekaru 12 jihar Borno ta tsara shirin da zai taimaka wajen kawo karshen ta’adanci a jihar ta hanyar karfafa guiwowin jami’an tsaro da kuma amsar tubar wadanda suka mika wuya.
“Samun tubabbun ‘yan Boko Haram 35,000 na daga cikin abubuwan da Allah ya yi mana kuma muke godiya a garesa a kullum muka wayi gari.
“Hakan na daga cikin addu’o’in da mutane suka rika yi da kokarin da jami’an tsaro suka yi da kira da shugabanin siyasa, sarakunan gargajiya, malaman addini suka rika yi domin a samu zaman lafiya a jihar.
Shugaban rundunar ‘Operation Hadin Kai’ a Arewa maso Gabas Christopher Musa ya ce ‘yan Boko Haram mutum 50,000 da iyalan su da mutanen da suka yi garkuwa da su sun mika wuya ga gwamnati.