Kamfanonin layukan wayoyin sadarwa a Najeriya sun bayyana cewa matsalolin da su ka dabaibaye su sun sa tilas in dai gwamnati ba ta yi wani abu a kai ba, to za su ƙara kuɗin kira da sauran amfanin da ake yi da layukan su.
Kamfanonin MTN, Airtel, Glo da sauran su, sun bayyana cewa matsalolin da su ke fuskanta sun haɗa tsadar yadda su ke gudanar da kasuwancin su da sauran hada-hada, waɗanda su ka haɗa da tsadar man dizel, tsadar amfani da jami’an tsaro masu kula da kayayyakin kamfani, yadda ake tsula masu haraji a wasu jihohi da sauran matsalolin masu yawa.
Shugaban Ƙungiyar Kamfanonin Layukan Waya Gbenga Adebayo, ya bayyana cewa matsalar tsadar man janareto a cibiyoyi da tashoshin injinan su ba ƙaramin cikas ya ke kawowa ba.
A Najeriya dai matsalar ƙaranci da tsadar man fetur da gas ta shafi harkokin cinikayya da na kasuwanci da hada-hada masu yawa.
“Mu na fama da tsadar mai kuma mu na fama da tsadar biyan masu tsaron ma’aikatan kamfanonin mu a jihohi daban-daban, har ma da masu tsaron kayayyakin mu a tashoshi daban-daban. Saboda haka idan gwamnati ta kasa magance waɗannan matsalolin, to fa tilas ne mu yi ƙarin kuɗi kawai.”
Ricikin Kamfanonin Layukan Waya Da Jihar Kogi:
Gbenga Adebayo ya ce ba gaskiya ba ne da Jihar Kogi ta ce ta na bin su bashi mai tarin yawa.
Maimakon haka, cewa ya yi ba ta bin su bashi, kuma Hukumar Tara Kuɗaɗen Harajin Jihar Kogi ta ƙaƙaba masu haraji daban-daban na ba gaira babu dalili.
Ya ce hukumar ta samu sammacin umarni daga kotu, an hana kamfanonin layukan waya isa a cibiyoyin su kusan 70, shi ya sa ake da matsalar yin amfani da layukan waya a jihar Kogi.
“Idan aka ci gaba a haka, ina tabbatar da cewa matsalar za ta iya shafar wasu sassan jihohin Kogi, Nasarawa, Benuwai, Enugu, Anambra, Edo, Ondo, Filato, Kwara da Neja har ma da wani yankin Abuja.”