Ofishin Kula da ‘Yan Gudun Hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNOCHA), ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 8.4 na buƙatar agajin abinci a Arewa maso Gabas.
Hukumar ta ce kashi 51.19 na yawan mutanen, wato mutum miliyan 4.1 ba su da cin yau, kuma ba su abin da za su ci gobe.
Ofishin na UNOCHA ya ce idan na a ɗauki matakan gaggawa ba, to yunwa za ta kwantar da su, har su kasa kataɓus. Haka dai hukumar ta yi gargaɗi.
Babban Jami’in Hukumar na Najeriya, Matthias Schmale ne ya yi wannan furucin a ranar Juma’a, wurin wani taro.
Kakakin OCHA Christina Powell, ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta aiko wa PREMIUM TIMES.
Ta ci gaba da cewa kashe-kashe sun haifar da rashin samun abinci mai gina jiki ga yara miliyan 1.74
Ta ce aƙalla ana buƙatar dala miliyan 351 domin samar da abinci da kayan agaji ga al’ummar yankin Arewa maso Gabas.
“Idan ba a taimaka wa waɗannan ɗimbin mutane da tallafi ba cikin gaggawa, to kuwa sakamakon haka za a samu yawaitar masu bada kan su ana lalata da su domin su samu abinci, ko kuɗin sayen abinci. Za a fuskanci masifar saka ƙananan yara cikin aikin ƙarfi domin neman abinci, wasu kuma za su sayar da ‘yan komatsan su ga ‘yan gwangwan.
Babban Sakataren Ma’aikatar Gona Ta Tarayya, Eanest Umakhile, ya ce mahara da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a yankin da kuma Arewa ta Tsakiya sun taimaka sosai wajen haddasa matsalar ƙarancin abincin a cikin wannan ƙasar.
Sauran waɗanda su ka yi jawabai a wurin har da Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta ce Birtaniya ta ce Birtaniya ba za ta gaji ba wajen bayar da tallafi domin magance matsalolin abinci da sauran matsalolin masu gudun hijira a Najeriya da Tafkin Chadi.
Wata Gagarimar Barazanar Yunwa:
Makonni biyu da suka gabata kuma Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), ta ce ‘yan Najeriya miliyan 19.4 za su fuskanci yunwa da barazanar rashin abinci a cikin Agusta, 2022.
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa aƙalla ‘yan Najeriya miliyan 19.4 ne za su yi fama da yunwa da barazanar rashin abinci tsakanin watannin Yuni zuwa Agusta, 2022.
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta yi wannan bincike tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da wasu Cibiyoyi masu ruwa da tsaki a harkar noma.
Rahoton ya yi nazarin matsalar ƙarancin abincin da za a fuskanta da kuma rashin abinci mai gina jiki a yankunan Sahel da Afrika ta Yamma.
Rahoton ya ƙara da cewa matsalar abinci za ta fuskanci aƙalla jihohi 21 na Najeriya tare da yankin Gundumar FCT Abuja, mai ƙananan hukumomi shida.
An kuma yi kirdadon aƙalla ‘yan gudun hijira 416,000 ne za su tsinci kan su cikin wannan mawuyacin halin tasku.
Sannan kuma rahoton ya nuna a yanzu haka aƙalla mutum miliyan 14.4 da kuma masu gudun hijira 385,000 sun afka cikin wannan halin rigimar gaganiyar ƙarancin abinci, kuma ba za su iya samun kan su a saiti ba, har sai cikin Mayu, 2022.
Jihohin da aka yi nazari a cikin Maris sun haɗa da Abiya, Adamawa, Benuwai, Barno, Cross Riba, Edo, Enugu, Gombe, Kaduna, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Legas, Neja, Filato, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara, dai kuma Gundumar FCT Abuja.
A cikin shekarar da ta gabata dai FAO ta ce aƙalla mutum miliyan 12.8 na ‘yan Najeriya su ka yi fama da fari na ƙarancin ruwan shuka tsakanin Yuni zuwa Agusta, 2021.
Matsalar tsaron da ta dabaibayi samuwar abinci sun haɗa da yaƙin Boko Haram a Barno, Adamawa da Yobe, sai kuma hare-haren ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, a jihohin Sokoto, Katsina, Zamfara, Kaduna da Kebbi. Sai kuma wasu jihohin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da Neja da Benuwai, waɗanda rahoton ya ce su ne lamarin zai fi yi wa riƙon laya a hannun ɗan dambe.
Sannan kuma rahoton ya ce matsalar tsadar kayan abinci da ya haddasa ƙuncin rayuwa a yanzu, zai ƙara ruruta wutar ƙarancin abincin sosai.
Sauran Matsalolin Da Ke Kara Ruruta Ƙuncin Rayuwa Da Rashin Abinci:
“Rashin aikin yi da suɓucewar aikin da mutum ke yi da kuma taguwar kuɗaɗen da magidanci ke samu sakamakon ɓarkewar korona, sai kuma fatattakar da ‘yan bindiga ke wa mutanen ƙauyuka da garuruwa su na yin hijira su zai ƙara kuma ya na ƙara munin matsalolin sosai.”
“Sauran dalilan da su ka sa matsalar ta 2022 za ta zarce ta 2021, shi ne saboda rashin hanyar isa wurin wasu masu gudun hijira da ke cikin lungunan Barno da Yobe, ƙarin munin hare-haren ‘yan bindiga da kuma ƙarin jihohi biyar da aka samu a cikin 2022.” Inji rahoton.
Wakilin Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) a Najeriya, Fred Kateero, ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya su yi amfani da sakamakon rahoton nan su shata wani tsari na ƙasa bai ɗaya, wanda zai bijiro da hanyoyin zabura a ceto harkar noma nan ba da daɗewa ba.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta zuba kuɗi sosai wajen tabbatar da samun nasarar wannan shiri.