Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Barno ta bada sanarwar kama lodin mota ɗauke da tulin albarusai, ciki har da na bindigar harbo jiragen sama har 126.
Wanda aka kama da albarusan dai wani mai shekaru 28, Clement Asuk, an damƙe shi ne a cikin tashar Maiduguri bayan ya loda kayan a motar haya.
Ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya na taimakawa a kai albarusan ne Jihar Kuros Riba, inda ya ce su na fama da yaƙi da ‘yan Awaren ƙabilar Igbo, wato IPOB.
‘Yan sanda sun ce a cikin tasha su ka kama shi a lokacin da ake ƙoƙarin ficewa da albarusan waɗanda ke danƙare cikin wata motar fasinja.
Albarusan masu ɗimbin yawa ne, har da albarusan harbo jiragen sama guda 126.
Ana amfani ne da bindigar nan girkakka da ake girkewa kan motar yaƙi wato RPG (Tashi-gari-barde).
Wannan ne karo na farko a tarihin yaƙin Boko Haram da aka taɓa kama irin waɗannan muggan albarusai a hannun wani mutum.
Sojojin Najeriya da ‘yan sanda sun sha kamawa kuma ana hukunta sojojin da aka samu da laifin sayar wa muggan ɓatagari makamai.
Asuk ya shaida wa jami’an tsaro cewa shi mazaunin jihar Benuwai ne, kuma zaman kasuwanci ya ke yi a can. Sannan kuma ya na da digiri na farko a fannin Fasahar Injiniya Jiragen Ruwa.
An samu nasarar damƙe Asuk bayan an samu rahoton sirri. An kama shi cikin Tashar Kano inda tuni har ya hau wata zungureriyar motar ‘yan safara (Luxurious bus), da nufin tafiya kudu.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Barno, Abdul Umar ya shaida cewa yayin da aka binciki kayan Asuk, an samu tulin muggan makamai a ciki, “waɗanda ka iya tayar da ƙaramin yaƙi.”
Albarusan Da Aka Kama A Tashar Mota:
Albarusan harbo jiragen sama guda 126.
Albarusai 222 samfurin 7.62.
Harsasai 517 samfurin 7.62 da kuma muggan gurneti-gurneti masu yawa.
Asuk ya ce shi ɗan aiken wani soja ne, wanda sojan ne ya aike shi kai makaman.
Ya ce sojan ya na aiki ne da Sojojin Operation Haɗin Kai, shi da wani farar hula da ya ce mai faɗa-a-ji ne a cikin ƙabilar su ta Ƙaramar Hukumar Kuros Riba. Ya ce sunan yankin ƙabilar ta su Obubra.
Premium Times ta buga labarin yadda ake yaƙi tsakanin IPOB da ‘yan yankin na Obubra.
Asuk ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wanda ya aike shi ya kai makaman na so su mallaki makaman ne domin su kare kan su daga hare-haren IPOB.
Ya ce su na maƙwautaka da Jihar Ebonyi, inda IPOB ke cin karen su ba babbaka.
An kama shi sanye da guraye da kambuna da karhunan tsatsube-tsatsube da ya ce ya ɗaura a jikin sa maganin ɓacin rana kada a kama shi.
Ya ce sunan sojan da ke da makaman ‘Lance Kofur Samuel, kuma shi ya damƙa masa makaman.
Ana ci gaba da bincike kafin a gurfanar da shi da dukkan sauran masu hannu a kotu.