Ɗan Majalisar Tarayya Ahmed Nasir daga Jihar Kano, ya yi kiran da a gaggauta tsige Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a Fannin Tsaro (NSA), Mohammed Monguno, saboda kasa shawo kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.
Nasir wanda ɗan APC ne, ya yi wannan kira a ranar Alhamis, a lokacin da ya ke bayanin karanta wani ƙudiri mai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa, wanda Ɗan Majalisa Shehu Balarabe daga Jihar Kaduna ya gabatar.
Ƙudirin da Balarabe ya gabatar shi ne ɗaukar matakan gaggawa dangane da kashe-kashen da ke faruwa a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.
Balarabe ya ce a mazaɓar da ya ke wakilta an kashe mutum 150.
Shi kuwa Nasir, cewa ya yi babu tsaro gaba ɗaya a faɗin ƙasar nan baki ɗaya, har ma a cikin Majalisar Tarayya kan sa.
“Shin wai mu na ma da Mashawarci a Fannin Tsaro kuwa?
“Mu na nufin Sojojin Sama da Sojojin Ƙasa da ‘Yan Sanda Sojojin Ruwa da DSS har da irin horon da suka samu a kasashen waje, amma a ce wasu ɓatagarin yara ‘yan shekaru 18 zuwa 18 sun fi su ƙarfi kenan?
“Ya Kakakin Majalisa, wannan mumnunan hare-hare da kashe-kashen sun isa haka nan. Tilas a kawo ƙarshen wannan tashin hankula.
“Ka hau mota a yi garkuwa da kai. Ka hau jirgin ƙasa nan ma a yi garkuwa da kai. Cikin makon jiya an kai farmaki a filin saukar jiragen sama. Ka zauna gida, a iske ka a gida, a yi garkuwa da kai. Ka aiki yaran ka a tare su a yi garkuwa da su.”
“Mai Girma Kakakin Majalisa, cikin makon jiya an yi garkuwa da wani mutum da suka ɗauke a asibiti. Shin ina za ka zauna ne. A cikin Majalisa ma za a iya shigowa har ciki ana iya shigowa a yi garkuwa da kai.” Inji Nasir.
“Shin me za mu cewa waɗanda su ka zaɓe mu? Shi ya sa yau ma na ke ƙara nanata cewa Mashawarcin Shugaba Buhari a Fannin Tsaro ba shi da wani amfani, a tsige shi kawai.”
Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Idris Wase, wanda ya jagoranci zaman, ya yi kira da cewa Majalisa ta yi ƙwaƙƙwaran bincike kan lamarin.
Idan ba a manta ba, a shekarun baya PREMIUM TIMES ta taɓa buga labarin yadda Monguno ya rubuta takardar zargin tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, marigayi Abba Kyari ya na kawo masa cikas wajen daƙile matsalar tsaron ƙasar nan.
Lamarin ya yi muni, har tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya haɗe kai da Abba Kyari, aka janye jami’an tsaron da ke ofishin NSA na Monguno.
Monguno ya ce an kashe biliyoyin nairori a zamanin su Buratai wajen sayen makamai, amma har yau lamarin sai ƙara muni ya ke yi
Daga baya ya nesanta kan sa daga rahoton.