Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da samun nasarar hana wani bam tashi a Rigasa, unguwar da tashar jirgin ƙasa ta ke a Kaduna.
Sun samu nasarar tone nakiyar ce (IED) bayan wasu masu kishi sun gaggauta kai rahoton ganin bam ɗin a ofishin ‘yan sanda.
“Mazauna unguwar ce suka ga nakiyar kuma suka gaggauta sanar wa ‘yan sanda.
“Yan sanda sun garzayawa wurin, kuma suka kwance bam ɗin bai ji wa kowa rauni ko kashe wani ba.
Da ya ke godiya ga mazauna yankin waɗanda suka ga nakiyar, Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Jalige ya ce tuni komai ya dawo daidai a unguwar ana ta harkoki da hada-hada.
Kwamishinan Harkokin Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya kuma ƙaryata ji-ta-ji-tar wai ‘yan bindiga sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna. Ya ce duk labarai ne na ƙanzon kurege kawai da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya.
Ya ce amma dai akwai lokacin da aka bada rahoton wasu ‘yan bindiga da suka tsere daga farmakin da sojoji ke kai masu ba ƙaƙƙautawa.
“Waɗannan ‘yan bindiga ne jami’an tsaro su ka bi su su ka nausa dajin Kasarani na yankin kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ya amince akwai ƙalubale na matsalar tsaro, amma jami’an tsaro daga ɓangarori da daban-daban su na ƙoƙari ba dare, ba rana domin samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Wakilin mu da ya bi hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Laraba, kwana biyu bayan harin da aka kai wa jirgin ƙasa, ya tabbatar da cewa tsakanin Bwari zuwa Katari babu jami’an tsaro ko ɗaya a cikin daji a ranar.
“A cikin Bwari dai akwai sojojin da ke binciken motoci a shingen tsakiyar gari. Da ka wuce su kuma ka kusa fita gari akwai jami’an VIO su na tare motoci. Daga nan babu jami’in tsaro ko ɗaya a tsawon tafiyar kusan minti 40 a cikin daji. Sai a Katari na ga motar ‘yan sandan mobal guda ɗaya, amma ban ga waɗanda ke cikin ta ba.