Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da kiraye-kirayen da Ƙungiyar Dattawan Arewa ta yi, inda ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, saboda kasa magance matsalar tsaron ƙasar nan.
Fadar ta ce ana kan fito da wani gagarimin tsarin tsaurara tsaro a faɗin ƙasar nan, nan ba da daɗewa ba.
Wannan bayani na cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.
Shehu ya ce murabus ɗin shugaban ƙasa ba shi ne mafita ba ga matsalar tsaron da ake fama da ita.
Ya ce tuni jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen daƙile ‘yan ta’adda, musamman a Jihar Kaduna da Neja da kuma yankin Neja Delta, kamar dai yadda Shugaban Ƙasa ya umarce su.
Garba ya ce ɓangarorin tsaro sun haɗa kai wajen ci gaba da farmakin yin galaba a kan masu haddasa matsalar tsaro, kuma ana ganin alamun nasara.
“Fadar Shugaban Ƙasa ba ta so ta na biye wa masu neman jan ta ana hauragiyar cika kafafen yaɗa labarai da maganganu, kamar yadda Kungiyar Dattawan Arewa ta yi, wato NEF
“Son neman a sani aiki ne na ‘yan siyasar da ba su ka kasa samun yardar talakawa masu zaɓe.
“Ya isa ta ɓangaren mu, mu fito mu ce murabus ɗin Shugaban Ƙasa a yanzu ba shi ne mafita daga matsalar tsaron da ƙasar nan ke fuskanta ba.
“A sani wannan matsala ce fa da ta daɗe shekara da shekaru ana fama da ita, daga nan kuma wannan gwamnatin ta gaje ta, bayan gwamnatocin baya sun yi watsi da ƙoƙarin daƙile ta.
“Ya na da muhimmanci ƙwarai jama’a su san irin ƙoƙarin da wannan gwamnatin ke yi, wajen ganin ta magance matsalar tsaro.
“Su kuma ‘yan siyasa ya na da kyau su sani kamata ya yi su taimaka ƙasa ta ɗore, ta yadda idan lokacin su ya yi, su ma su sami wurin da za su yi wa mulki.
“Saboda idon mutum ya rufe da neman mulki, bai kamata ya tarwatsa ƙasar ya ke son ya ɗare kan mulkin ta ba.
“Ma’aikatar Tsaro na bakin ƙoƙarin ta wajen ganin cikin gaggawa kwanan nan ta fito da tsare-tsare da kuma kai farmaki a yankunan Kaduna da Neja, kamar yadda Shugaba Ƙasa ya ba su umarni.
“A wurin Taron Majalisar Zartaswa na ranar Taraba, an amince a sayo tulin makaman da ba a taɓa a taɓa kawo masu yawan su ba a lokaci guda.”
Ya ce a yanzu haka ana samun gagarimar nasara, ana kama ɗimbin masu hana ƙasar nan.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta cika alƙawarin ta na samar da dawwamammen zaman lafiya a faɗin Najeriya.