Daga ranar 10 zuwa 16 ga watan Afrilu 2022 ‘yan bindiga sun kashe mutum 215 a Najeriya.
A lissafe ya nuna cewa akalla mutum 30 ne ake kashewa duk rana a makon.
A makon jiya ‘yan bindiga sun kashe mutum 142 a jihar Filato, mutum 26 a Ebonyi sannan mutum 23 a Benue.
Akwai ‘yan sanda 4 daga cikin yawan mutanen da aka kashe.
PREMIUM TIMES ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 2,968 a cikin watanni uku da suka gabata a kasar nan.
An Kuma samu karuwa a yawan mutanen da ‘yan bindiga ke kashewa a kasar nan a makon da jiya fiye da makonnin baya.
Arewa maso Yamma
‘Yan bindiga sun kashe dagacen kauyen Kaura dake karamar humumar Chikun a jihar Kaduna Isiaku Madaki tare da wasu mutane 14.
‘Yan bindigan sun kashe wadannan mutane a ranar Litinin din da ya gabata da safe.
Wani mazaunin kauyen Baban David ya ce ‘yan bindiga sun kashe dakacen bayan ya yi kwanaki biyu da zama dakace a kauyen.
Kudu maso Yamma
‘Yan bindiga sun kashe shugaban jami’an APC dake karamar hukumar Atakumosa na Gabas na Tsakiya a jihar Osun.
Maharan sun kashe Gbenga Ogbara ranar Litinin da ya gabata a cikin gidan sa dake kauyen Igangan.
Kudu maso Gabas
A ranar Litinin din da ya gabata ‘yan bindiga suka kashe mutum daya sannan suka cinawa wa mota mai kiran ‘Toyota Sienna’ wuta a shatale-talen Holy Ghost dake karamar hukumar Enugu ta Arewa a jihar Enugu.
Ana zargin cewa ‘yan kungiyar IPOB ne suka aikata haka.
IPOB sun kai wa mutane hari wai don sun karya dokar zaman gida dole da kungiyar ta saka a jihar.
‘Yan kungiyar sun kuma kwace mota kiran Bus a harin.
A ranar Laraban da ta gabata ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu a ofishin ‘yan sanda dake kauyen Atani dake Ogbarujihar a jihar Anambra.
Jami’in hulda da jami’a na rundunar Tochukwu Ikenga ya ce maharan sun far wa ‘yan sandan da misalin karfe 11 na safe.
Daga nan bayan an yi awa 24 maharan sun kara Kkai wa ofishin ‘yan sanda dake kauyen Nteje dake karamar hukumar Oyi da misalin karfe 3 na ranar Alhamis.
‘Yan sandan sun yi bata kashi da maharan inda suka kashe daya daga cikinsu.
A jihar Ebonyi ‘yan bindiga sun kashe wani babban dan kasuwa Issac Chukwu a Abakaliki.
Chukwu ya gamu da ajalinsa ana sauran sati daya a daura masa aure ranar Litini.
‘Yan bindiga sun kashe mutum 26 kauyen Effium/Ezza-Effium dake karamar humumar Ohaukwu ranar Lahadi da safe.
A jihar Imo hukumar INEC ta dakatar da yi wa mutane rajistan katin zabe a wata karamar hukuma bayan an kashe jami’in hukumar.
‘Yan bindigan sun kashe Nwokorie Anthony dake aiki a kauyen Nkwo Ihitte mazabar Amakohia a karamar hukumar Ihitte Uboma ranar Alhamis.
Mutum hudu sun ji rauni a dalilin harin.
Arewa ta Tsakiya
‘Yan bindiga sun kashe mutum 142 a wasu kauyukan dake kananan hukumomin Wase da Kanam.
Mahara sun kai hari kauyukan Kukawa, Gyambawu, Dungur, Kyaram, Yelwa, Dadda, Wanka, Shuwaka, Gwammadaji da Dadin Kowa ranar Lahadi.
Bayan kwanaki uku wani dan majalisan wakilai na jihar dake wakiltan yankin ya ce ‘yan bindigan sun kashe mutum 92 sannan daya daga cikin masu taimakawa gwamnan jihar ya ce maharan sun kashe mutum 142.
A jihar Benue ‘yan bindiga Wanda ake zargin cewa Fulani makiyaya ne sun kashe mutum 23 a wasu kauyuka biyu a jihar.
‘Yan bindiga sun kashe mutanen a kayukan Mbadwem da Tiortyu dake kananan hukumomin Guma da Tiortyu ranar Litini.
Arewa maso Gabas
‘Yan bindigan sun kashe dakacen kauyen Maisamari dake karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba Abdulkadir Sufiyanu.
Mazaunan kauyen sun ce ‘yan bindigan sun kashe dagacen a wajen karfe 8 na dare a masallaci lokacin yana sallar Asham.