Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa mako ɗaya bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin ƙasa a cikin dajin Kaduna, a halin yanzu dai fasinjojin da ba san halin da su ke ciki ba, sun kai 168.
Shugaban Hukumar Jiragen Ƙasa Fidet Okhiria ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Premium Times ta bayar da sanarwar hatsarin jirgin, wanda aka tabbatar da cewa mutum 8 aka kashe, aka tsere da mutum 22, daga cikin fasinjoji 362 da aka haƙƙaƙe a rubuce na cikin jirgin.
Sai dai kuma mutane da dama sun haƙƙaƙe cewa mutanen da ake cikin sun fi yawan 362, idan aka yi la’akari da irin cuwa-cuwar da ma’aikatan jirgin ke yi wajen ɗora fasinjoji su na danna kuɗaɗen a cikin aljifan su.
NRC ta ce zuwa yanzu an ƙara tabbatar da cewa wasu fasinjoji 14 daga cikin waɗanda ake cigiya, lafiyar su ƙalau.
“Saura 176 ake nema, waɗanda a cikin su an tabbatar da kama 22 da kuma mutuwar mutum 8.
Adadin waɗanda ake cigiya a yanzu ya kai fasinja 168, waɗanda tun bayan afkuwar farmakin, ba amo kuma ba labarin su.
“Daga cikin fasinjoji 168 da ake cigiya, an tabbatar da cewa 22 na hannun ‘yan bindiga. Wayoyin wasu 51 duk a kashe su ke tun bayan da aka kai wa jirgin mummunan hari.
“Akwai kuma lambobin wayoyi har guda 35 waɗanda idan an buga su na ƙara, amma tsawon mako ɗaya ba a ɗagawa ballantana a amsa kiran. Wasu 22 kuma iyalan su ne su ka tabbatar da cewa ba su san inda su ke ba.”
Okhiria ya ce zuwa yanzu an ceto taragai bakwai waɗanda ya ce duk an ƙarasa da su Tashar Jiragen Ƙasa ta Rigasa, Kaduna.
Ya ce ana nan ana ci gaba da aikin gyara titin jirgin domin ya ci gaba da jigila a tsakanin Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Abuja.
Discussion about this post