Tsohon gwamnan Kgaz RabiuKwankwaso ya siya fom ɗin takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyya mai alamar kayan daɗi har naira miliyan 30.
Kwankwaso ya siya fom ɗin ne a ofishin jam’iyyar dake Abuja ranar Talata.
Shugaban jam’iyyar NNPP ta kasa Farfesa Rufai Alkali tare da babban jami’in tsare-tsare na jam’iyyar Sanata Suleiman Hunkuyi ne suka tarbi tsohon gwamnan sannan suka biya.
Yayin da yake jawabi jim kadan bayan ya karbi fom din, Kwankwaso ya ce jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APC da jam’iyyar adawa ta PDP ba su da sauran rawan da za su taka domin ‘yan Najeriya sun gwada su kuma sun gaza.
Ya hori ƴan Najeriya da su karkata zuwa jam’iyyar NNPP a zabukan da ke tafe domin cigaban kasa.