Wani abu da ya zame wa mutanen Najeriya musamman a yankin Arewacin Najeriya annoba yanzu shine wani magani da aka kirkiro shi mai suna ‘Kurkura’.
Kurkura wata aba ce da ake siyarwa a musamman shagunan siyar da magungunan gargajiya, wasu da dama da ake kira ‘Islamic Chemist’ anan ne ake samun wannan magani da ake kira ‘Kurkura’.
‘Kurkura’ ruwan magani ne da ake saida shi a cikin ‘yar karamar kwalban magani wai tana maganin kowani irin cuta. Sun yi mata lakabi da suna ‘Antibiotics’
Wannan magani ya zama annoba domin ba yara matasa ba kawai harta magidanta, malamai, ‘yan kasuwa, direbobi da sauransu kowa yana amfani da wannan magani ‘Kurkura’.
Duk mai shan maganin zai rika cewa wai magani ne da yake masa aiki wajen magance cutar sanyi, basir, amosani, da dai duk wata cuta dake damun mutum.
Babbar abin tashin hankali ga wannan magani ‘Kurkura’ shine daga ka fara yin shi shikenan ka kamu. Baka iya rayuwa sai da shi. A kowani hali kake za ka bukaci kurkura domin ka rayu.
Wani mashayin Kurkura da ya zanta da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya bayyana cewa a kullum yanayin kurkura sama da sau 10.
” Ina yin kurkura sama da sau 10 a rana. Tana sa in ji garau sannan yan cututtukan da na kan ji a jiki na duk ban jin su idan na yi kuskura.
Wannan matashi mai suna Garba Hassan, ya ce abin ya zamo masa jiki dole yayi shi.
Yadda mashayin kwaya, Wiwi, Sigari da sauransu ke fadin sabo ya ke saka su ba su iya barin shaye-sahaye haka mai yin kurkura zai ce bashi iya bari idan ya fara yi.
Tanimu Albarka, ya tabbatar wa wakilin mu cewa tabbas akwai wadanda suka rasu a dalilin yin kurkura a lokacin farko yin su.
” Babu wani da zai ce maka bai kusa shekawa lahira ba da yayi wannan Kurkura da farko a rayuwan sa. Idan fa ka yi zaka afka cikin rudani ne da tashin hankali na take. Za ka yi ta kwarara amai, wasu har da zawo su ke yi, mutum ya kan fadi warwas ne rai a hannun Allah.
” Amma kuma a haka mutane suke yi har su saba. Akwai wadanda ya zo musu da karewar kwana. Daga yin su sai kabari.
Yadda ake yin kurkura
Albarka ya bayyana cewa shi ruwan wannan magani kurbarsa a ake yi a kuskure baki. Shikenan, ” Amma kuma fa daga lokacin da ka rike shi a cikin bakinka zai fara aiki.
Mutane da dama da suka zanta da wannan Jarida sun bayyana cewa sun saba barin su sai Allah.
Wani mai shagon saida Kuskura ya bayyana cewa suma sukan siyo shi daga yankin kudu ne. Wato daga can kudu ake siyo shi a hada mutane kuma su yi ta kurkura.
Wani matashi mai suna Awwal Sani, ya ce shi dai abin ya ishe shi yanzu ya zama masa annoba da bala’i. “Ni ban taba shan taba, wiwi ko kwaya ba amma na afka harkar kurkura gashi yanzu dole sai na yi kurkura nake iya jin dadin jiki na da rawuya ita kanta. Wanna bala’i har ina. Ina rokon Allah ya sa in iya barin sa yanzu.
Sheikh, Ibrahim Disina na talbijin din Sunnah Tv, ya amsa wata tambaya da aka yi masa game da yadda mutane suka karkata wajen yin amfani da Kurkura yanzu, amsar sa kuwa itace , ko a musulunci wannan abu bai halatta ba saboda ya na daga cikin nauyin abin da zai jirkita lafiya da tunanin mutum kuma musulunci ya haramta haka.
Wani malamin asibiti da ya zanta da PREMIUM TIMES Hausa ya ce kwaya ce kawai da za ta illata mutane nan gaba. ” Domin ko maganin da ake ce wa Anti-biotics a asibiti ana ba da shi ne bayan anyi gwaji sannan kuma na wani lokacine za a sha daga nan kuma sai a barshi. Amma wannan abu wai kurkura da zarar mutum ya fara shi kenan ya afka cikin sa kenan sai wada hali yayi.
Yanzu dai Kurkura ita ce ke kan gaba wajen dibar mutane a yankin Arewa. Duk lungu, kwararo, sako, gidaje, shaguna, ko ina ana saida kurkura. da zarar ka gamu da mutum bakin sa a kunshe yana maka magana da kyar, toh yana kunshe ne da ruwan maganin.