A daidai kowa na bayyana ra’ayin sa na fitowa yin takarar shugabancin Najeriya, ƴan ƙabilar Igbo mazauna jihohin Arewacin Najeriya kaf ɗin su sunce ministan kwadago, Chris Ngige su ke so ya zama shugaban kasa a 2023.
Shugaban kungiyar ƴan kabilar Igbo mazauna yankin Arewa Chief Chi Nwogu ya ce wannan shawara ce wanda gabaɗayan su suka amince da shi.
” Lokaci yayi da ɗan ƙabilar Igbo zai ɗare kujerar shugabancin Najeriya. Mun gaje da zama kullun tayan baya. Shugabancin muke so kuma Ngige ne zaɓin mu.
Nwogu ya kara da cewa duk cikin ƴan takaran da suka fito daga yankin babu kamar Nigige.
” Ku je ku duba tsawon lokacin da yayi mulkin jihar Anambra, har yanzu ayyukan da yayi ne ake cin moriyarsu a jihar.
” Saboda haka, ganawa da yake yi da neman shawara ya isa haka ya fito kawai ya bi sahun sauran yan takaran a fafata shi, domin shi muke so.
An gudanar da wannan taro ne a babban birnin tarayyar Nigeria, Abuja ranar Asabar.
A cewar kakakin ministan, shugaban ƴan ƙabilar Igbo mazauna jihar Bauchi Eze-Ndigbo Bauchi, Jude Umezika ya ce tabbas idan jagora ake nema daga yankin kudu maso gabashin ƙasar nan Ngige ne ya fi dacewa da cancanta gabaɗaya ƴan ƙabilar su karkata zuwa ga su mara wa baya.