Kotu a Gwagwalada Abuja ta yanke wa Adama Bello hukuncin biyan tara har naira 200,000 a dalilin zargin makwabciyarta Zainab Samaila da tayi da maita.
Alkalin kotun Sani Umar ya ce Adama za ta gabatar da shaida daya wanda zai kawo wa kotu fasfo dinsa biyu.
Ya ce shaidan da Adama za ta gabatar zai ba da adireshin gidansa da yake zama a wurin da kotun ke da Iko.
Umar ya ce Saba wa sharuddan da ya bada zai sa a daure Adama a kurkukun Suleja.
Lauyan da ya shigar da karar ya bayyan cewa ‘yan sanda sun kama Adama wacce ke zama a Yangoji a Kwali bayan Zainab ta kai kara ofishin ƴan sanda ranar 6 ga Afrilu.
Tanko ya ce Adama ta zargi makwabciyarta Zainab da maita tun a watan Fabrairu.
“A wannan watan ne Adama ta haihu inda ita Zainab ta bata kyautar kwalban manja daya da naira 200 domin murnar sauka lafiya.
“Bayan an yi kwanaki sai Adama ta fito tana zargin Zainab cewa ita mayya ce kuma ta so ta kashe ta.
Ya ce Zainab ta yi rekodin din Adama yayin da take zargin ta da maita wanda aka gabatar a kotu.
Sai dai kuma Adama ta musanta waɗannan zage-zage a gaban alkali.
Alkali Umar ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 14 ga Yuni.
Discussion about this post