Kwamitin Tsarin Karɓa-karɓa na jam’iyyar PDP ya watsar da batun ware ɗan wata shiyya cewa shi zai fito takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2023.
Kwamitin mai mambobi 37 da ke ƙarƙashin shugabancin Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom, ya amince cewa ko ɗan wane shiyya a ƙasar nan zai iya fitowa neman kowane muƙami a takarar zaɓen 2023, har da zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Sun zartas da haka ne a taron da suka gudanar ranar Talata a Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Idan Kwamitin Zartaswa na uwar jam’iyya ya amince da wannan matsaya, to PDP ba za ta ware kudu ko arewa kaɗai ko wata shiyya a ce sai daga can ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito ba.
Duk da Ortom bai fito fili ya bayyana cewa sun rushe karɓa-karɓa ba, amma dai ya ce matsayar da suka cimma za su je su miƙa ta ga uwar jam’iyya domin amincewa.
“Amma kuma majiyar Punch ta ce kwamitin duba yiwuwar karɓa-karɓa ya soke tsarin “saboda rashin wadataccen lokaci.”
Cikin watan Maris ne Shugaban PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu ya kafa kwamitin mai mambobi 37.
Idan ba a manta ba, shugabannin Kudu maso Gabas na tayar da jijiyar wuya cewa sai ɗan yankin su zai yi shugabanci a 2023.
Sun ce tun da ake zaɓe, ɗan ƙabilar Igbo bai taɓa yin shugabanci ba.
Su ma gwamnonin kudu sun ce tilas sai dai mulki ya koma kudu a 2023.
A ɓangaren Arewa kuwa, dattawan ta na kafa hujja da cewa a shekaru 16 da PDP ta yi mulki, shekaru 14 duk ‘yan kudu ne suka yi mulki, wato Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan. Sai fa marigayi Umaru ‘Yar’Adua da ya yi shekaru biyu da watanni. Don haka sai dai ɗan Arewa ya tsaya wa PDP takara a 2023 kenan.
Tuni dai sai ‘yan takarar shugaban ƙasa ke ƙara bayyana a ƙarƙashin PDP, kama daga Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma da Kudu Maso Kudu.
A Arewa akwai irin su Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal, Bala Mohammed, Bukola Saraki da Mohammed Hayatuddeen.
Discussion about this post