Dattijo Wole Soyinka ya yi tir da yadda jam’iyyar APC ta zaɓi Iyiola Omisore Sakataren Jam’iyya na Ƙasa, mutumin da aka taɓa ɗaurewa bisa zargin hannu a kisan tsohon Ministan Shari’a, Bola Ige.
Soyinka ya nuna fushin sa ne ganin cewa an zaɓi Omisore Sakataren APC watanni uku bayan an sake buɗe fayil ɗin binciken kisan na Bola Ige, wanda ake zargin Omisore da hannu ciki.
“To yanzu dai babban wanda ake zargi da hannu a kisan Bola Ige ya zama Sakataren APC jam’iyya Mai mulki. Shin ko Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya zai iya fuskantar shingayen siyasar da za su iya tare masa gaba idan an ci gaba da binciken?
“Shin ko akwai garanti cewa sakamakon binciken da za a gano za a iya fito da shi don kowa ya gani?” Tambayar da Soyinka ya yi kenan.
An dai bindige Bola Ige a ranar 23 Ga Disamba, 2001, shekaru 21 da suka gabata.
A lokacin taron tunawa da cikar sa shekaru 20 da mutuwa, Soyinka ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cika alƙawarin da ya ɗauka cewa zai sa a sake gudanar da binciken musabbabin kisan Ige, domin a hukunta masu laifi a kisan sa.
Omisore ne babban wanda aka fi zargi a kisan, kuma har ‘yan sanda su ka tsare shi tsawon watanni da dama. Sai daga baya aka sake shi.
Sai dai kuma ya sha ayyana cewa ba shi hannu a wannan kisan.
Soyinka ya ce bayan ya yi kira ga Shugaban Ƙasa, nan da nan Buhari ya amsa kira ta hanyar umartar Sufeto Janar ya sake buɗe fayil ɗin kuma zuwa yanzu kafin a fito da sakamako, Omisore ya zama sakataren jam’iyar APC na Ƙasa.
Dalili kenan Soyinka ke ƙorafin cewa hakan da aka yi zai sa jama’a yin tantama idan an fito da sakamakon binciken, musamman idan aka wanke Omisore.
“Sannan kuma duk alƙalin da ya samu kan sa cikin irin wannan yanayin, to za a riƙa zargin sa ƙwarai da gaske.
Idan ba a manta ba, Iyiola Omisore ya taɓa cin zaɓe a lokacin da ya ke tsare a kurkuku.
Ana kuma raɗe-raɗin cewa an saka masa da muƙamin sakataren APC ne saboda goyon bayan da ya bayar a zaɓen jihar Osun inda ya zo na uku a ƙarƙashin SDP, har APC wadda ta zo ta biyu, ta kayar da PDP wadda ta zo na ɗaya, a lokacin kammala wata rumfar zaɓe guda ɗaya da INEC ta ce sai an sake zaɓen waccan rumfa.
Discussion about this post