Mutanen ƙauyen Gidan Daudu sun ga tashin hankali da dare a ranar Talata, yayin da ‘yan bindiga su ka darkaki garin, suka kashe babban attajirin da ake taƙama da shi.
Maharan waɗanda su ka je a kan babura ɗauke da zabga-zabgan bindigogi, sun darkaki gidan Sale Auta wajen ƙarfe 9 na dare, suka fito da shi waje, sannan suka bindige shi.
Majiya ta tabbatar wa wakilin mu cewa maharan sun yi gaba da wata ‘yar Sale Auta, mai suna A’isha da kuma wasu mutum bakwai.
Auta dai ɗan kasuwa ne, kuma ƙasaitaccen attajirin ƙauye da ke Gidan Daudu.
Washegari Laraba ne wani mazaunin Ƙanƙara mai suna Magaji Basiru, ya shaida wa wakilin mu cewa, “maharan dama takakkiya su ka yi wa wanda suka kashe ɗin.”
“Misalin ƙarfe 9 na dare suka isa ƙauyen. A lokacin ni ina Ƙanƙara. Sun kutsa cikin gidan sa kuma suka fito da shi waje, sannan su ka bindige shi.
“Kuma sun kama wata ‘yar sa budurwa, mai suna A’isha, tare da mutum bakwai duk suka yi gaba da su.”
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina Gambo Isa ya shaida wa wakilin mu cewa zai bibiyi lamarin sannan ya kira shi. Sai dai har lokacin haɗa wannan labarin bai waiwaye shi ɗin ba.
Jihar Katsina na sahun gaba cikin jihohin da zaman lafiya ya gagara a wasu ƙananan hukumomi masu yawa shekaru da dama.
‘Yan bindiga na addabar yankunan jihar da hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane ana biyan ɗimbin kuɗin fansa.
Dubban ɗaruruwan mutane a jihar Katsina sun yi gudun hijira saboda farmakin da ake kai masu.
Wasu yankuna da dama noma ya gagara, kuma ana kama matan aure da ƙananan ‘yan mata ana nausawa da su cikin daji ana lalata da su tsawon kwanaki ko watanni.
Sai dai kuma duk da haka, kwanan baya ne Gwamna Aminu Masari na jihar ya ce ba a taɓa samun gwamnatin da ta kawo wa talakawa alheri, kamar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba.
Discussion about this post