Duk da irin ragargazar da ‘yan bindiga su ka yi wa garuruwa da ƙauyukan Jihar Katsina, kisan dubban jama’a, tarwatsa su zuwa gudun hijira da garkuwa da dubban mutane da biyan biliyoyin kuɗaɗen fansa, musamman a Katsina da Zamfara, Gwamna Aminu Masari ya bayyana cewa Najeriya ba ta taɓa dacen shugaba mai kulawa da ‘yan ƙasar kamar Buhari ba.
Masari ya sha nanata cewa matsalar tsaro ta ci ƙarfin jihar sa, ‘yan bindiga sun fi ƙarfin jami’an tsaro, don haka kowa ya tashi ya kare kan sa.
Sai dai kuma duk da wannan mummunan hali da yanki Arewa maso Yamma ya faɗa, musamman Jihar Katsina, Masari ya fifita mulkin Buhari bisa na duk sauran shugabannin da aka taɓa yi a tarihin kafuwar Najeriya.
“Daga lokacin da aka haɗe kudu da arewacin ƙasar nan cikin 1914 har aka samar da Najeriya zuwa yau, ba a taɓa yin dacen shugaban ƙasa kamar Buhari ba.”
Masari ya yi wannan furucin ne a wurin taron gangamin da waɗanda su ka ci moriya da gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na NSIP su ka shirya a Katsina.
An shirya shirin ne a ƙarƙashin ƙungiyar SPGFVI, bisa jagorancin kodinetan ta Mustapha Bara’u.
Masari ya ce Shugaba Buhari ya cancanci zama shugaban da a tarihin Najeriya ba a taɓa yin dacen shugaba kamar da ba, irin shirye-shirye na inganta rayuwar al’umma, musamman marasa galihu da ya bijiro da su.
Ya ce idan aka riƙe waɗannan shirye-shirye bayan wa’adin mulkin Buhari su ka ɗore, to ‘yan Najeriya sun kama hanyar fita daga rukunin masu fama da talauci kenan.
Masari wanda ‘yan bindiga sun tarwatsa ɗaruruwan ƙauyuka a jihar sa, har sai da ta kai wasu na tsallakewa gudun hijira a Jamhuriyar Nijar, wasu na hijira su na komawa Kano ɗungurugum, duk da haka ya ce ba a taɓa samun shugaba kamar Buhari ba.
Ya goyi bayan wannan shiri ya kasance Majalisar Tarayya ta kafa dokar maida wannan shiri na dindindin.
Daga nan ya umarci waɗanda su ka shirya gangamin cewa su isar da saƙon su har ga wakilan ƙananan hukumomin su da ke Majalisar Tarayya.
Dama kuma kodinetan SPGFVI, Mustapha Bara’u, ya ce babban dalilin shirya gangamin wanda aka rigaya aka fara yi tun a ƙananan hukumomi, shi ne a yi kira da a maida shirin na dindindin.
Ya ce shiri ne da matasa, maza, mata, dattawa tsoho da tsohuwa da masara galihu da naƙasassu ke matuƙar amfana da shi.