Amurka ta bada sanarwar amincewar sayar wa Najeriya jiragen yaƙi da sauran makamai. Za a yi amfani da jiragen yaƙin wajen kakkaɓe Boko Haram da ‘yan bindiga waɗanda suka addabi ƙasar, musamman Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Hukumar Tsaron Amurka ce a ranar Alhamis ta bayyana cewa kayan yaƙin za su kai na dala miliyan 997.
Ana ƙoƙarin sake kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗen ne ƙasa da shekara ɗaya bayan Amurka ta kawo wa Najeriya jiragen yaƙi 12 samfurin Tucano, waɗanda tuni Najeriya ta biya kuɗaɗen su.
Tun cikin watan Yuli, 2021 Amurka ta fara kawo jiragen Tucano 6, wanda aka biya a wancan tsohon ciniki.
Sabbin Makamai Daga Amurka:
Bayanin da Amurka ta fitar a ranar Alhamis ya tabbatar da cewa sun kunshi:
1. Helikwaftan kai farmaki guda 22, samfurin AH-1Z.
2. Injinan helikwaftan yaƙi 28.
3. Zabga-zabgan bindigogi guda 2,000, samfurin tashi-gari-barde masu ɗauke da na’urorin hangen nesa.
Sauran sun haɗa da na’urorin Hangen Abokan Gaba A Cikin Duhu (NVCD),
Akwai kuma mashinga, kayan gyaran jirage da na gyaran makamai, kwantinonin zuba injina, kayan gwaji da sauran kayayyaki da manyan makamai masu tarin yawa.
Sanarwar ta ce a cikin kuɗin kwangilar akwai ladar biyan yadda za a yi wa jami’an tsaron Najeriya horon yadda za su iya sarrafa makaman.
“Sayar da waɗannan makamai Ga Najeriya zai kasance wata gudummawa ga ƙasar wajen shawo kan matsalar tsaro a ƙasar.”
Sanarwar ta ƙara da cewa za a shafe shekaru biyar ana koya wa rukuni-rukunin jami’an Najeriya dabarun gyaran jiragen da sauran na’urori da manyan makaman.
Amma da farko za a ɗauki kwangilar kamfanoni uku ne da za su shafe shekaru biyu na farko a Najeriya su na koya dabarun kula da kuma gyaran kayan yaƙin.
Za a sayi waɗannan kayan yaƙi shekara ɗaya kafin ƙarshen mulkin Buhari, kuma a daidai lokacin da ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram ɓangaren Ansaru ke ƙara ƙarfi a Arewa.
A farkon makon jiya ne kuma Majalisar Tarayya ta yi tambayar cewa me ake yi da maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa a fannin tsaro, tun da kashe-kashe da garkuwa da mutane da sauran nau’ukan hare-hare sai ƙaruwa su ke yi, maimakon a ga alamun su na raguwa.