Biyo bayan ihu da kwaroronton da ake yi akan saki da gwamnati Mai ci ta Shugaba Buhari tayi na amincewa da sakin tsoffin gwamnonin kasar nan guda biyu; wato jolly Nyame na Taraba da Kuma Joshua Dariye na Plateau bayan zargin da hukucin da kutu ta zartar musu na zaman gidan kaso.
A zaman da Shugaban kasa Mai ci a yanzu ya shugabanta Wanda ya hadar da manyan kasar nan masu fada aji da tsaffi da masu ci a mulkin kasar nan wato state council .
Sun roki Shugaba Buhari da yayiwa Allah ya saki wadanan tsaffin gwamnonin guda biyu da aka ambata a baya duba da yanayin da lafiyarsu ke ciki. Amincewar da gwamnati tayi ya bar baya da kura shi ne nake son tunawa mutane cewa ba a wannan gwamnatin irin hakan ta fara faruwa ba misali: A ranar 25 ga watan oktoba na shekarar 2009 kotu ta daure Alh Aminu Dabo da chif Bode George shekara 28 bayan tuhumarsu da yin sama da fadin naira biliyan 84.
Bayan shafe wasu lokuta a daure tsohon Gwamnan kano Rabiu Musa shi ne ya shige gaba aka da roko da lallami gurin Shugaba mai ci a wancan lokacin ya Kuma samu aka saki Alh Aminu Dabo a wancan lokacin aka Kuma sake shi a 2 ga watan June na shekarar 2011.
A ranar da ya fito ya samu kyakkywar tarba daga kanawa masu tarin yawa Wanda su ka raka shi a gidansa.
Mutum na biyu da ya amfana da irin wannan alfarma ko affuwa shi ne Muhammad Abacha Wanda shi ma kotu ta daushe shi shekara 25 daga baya aka sassauta hukuncin zuwa shekara 15 Wanda shi ma tsohon Gwamnan jahar kano Alh Rabiu Musa Kwankwaso ne ya shige gaba wajen fitowar sa a ranar 24 ga watan saftamba na shekarar 2002.