Kwwmishinan ƴan sandan jihar Kaduna Yekini Ayoka ya bayyana ce jami’an tsaro sun yi kuskure wasu makiyaya da ke bin sawun shanun su da aka sace a matsayin ƴan bindiga.
Idan ba a manta ba an rika yaɗa wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna wasu mutane da dama sojoji na jejjefa su cikin mota a matsayin ƴan bindiga suna kama.
Bayan bincike da aka gudanar an gano ashe jami’an tsaro sun yi kuskure ne. Waɗanda suka kama babu abinda ya haɗa su da ta’addanci, hasali na sun fito ne neman shanun su da ƴan bindiga suka sace musu.
” An tafka kuskure matuka domin a gaskiya waɗannan mutane da aka rika jejjefawa cikin mota ba ƴan bindiga bane. Suma hari aka kai musu aka sace musu shanu, shine suka fito neman shanun su.
” Sun yi arangama da ƴan kungiyar banga na kauyukan Kakura da ke karamar hukumar Chikun a cikin daji a lokacin da suma suka biyo sawun ƴan bindigan. Sun yi batakashi a tsakanin su kafin daga baya aka kane ashe suma ƴan bindigan suke nema.
” Daga nan ne jami’an tsaro suka dira dajin inda suka kama su duka suka rika loda su a bayan mota.
Kwamishina Yekini ya ce tuni an garzaya da waɗanda suka ji rauni asibitin sojoji na 44 domin a basu magani.
Fitaccen malami Sheikh Ahmed Gumi, ya karanta wasika daga kungiyar Fulani makiyaya a lokacin karatun tafsiri inda ya ke bayyana rashin jin daɗin su bisa cin mutuncin da jami’an tsaro suka yi musu duk da ko cewa suma suna fama da hare-haren ƴan bindigan ne.
Gumi ya ce jami’an tsaro ba su nuna kwarewa a abinda suka aikata ba.
Discussion about this post