Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba sani ba sabo a zaben fidda dan takarar shugaban kasa da za a yi a cikin watan gobe.
Jam’iyyar ta ce ba za a yi maslaha ba kowa ya wasa wukar sa kawai a dira filin yanka, wanda ya iya fawa wa kwashi babban rabo, ya cira tutar jam’iyyar a zaben 2023 dake tafe.
Wannan yana kunshe ne cikin matsayar da jam’iyyar ta dauka yayin taron majalisar zartarwarta, a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam`iyyar na kasa da jihohi da gwamnoni da sauran jiga-jiganta na kasa baki daya.
Bayan haka jam’iyyar ta sanar da siyar da fom din takarar kujerun ta kamar haka:
Shugaban Kasa naira miliyan 100. Kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30, fom naira miliyan 70
Gwamna naira miliyan 50
Sanatoci naira miliyan 20.
‘Yan majalisar wakilai naira miliyan 10.
‘Yan majalisar jiha naira miliyan biyu.