Tsohon gwamnan Kano sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar APC mai mulki babu inda ya tafi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwar da ya saka wa hannu kuma ya fitar ranar Litinin.
Shekarau ya ce ” Labaran da ake yadawa cewa ina shirin canza sheka zuwa wata jam’iyya ba gaskiya bane. Ni Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano ina nan a cikin jam’iyyar APC, babu wani shiri ko kulli a sarari ko a boye na shiga wata jam’iyya ta daban.
Ga cikakken bayani a nan:
Assalamu alaikum
Ina yi wa dukkan al’ummar Najeriya Barka da Shan Ruwa. Ina fata Allah SWT ya karbi ibadunmu.
A kwanakin nan na goman karshe a Ramadan muna rokon Allah ya sada mu da wannan dare mai daraja na Lailatul Qadri.
Daga safiyar jiya zuwa yammacin yau Lahadi 24 ga watan Afrilu 2022 na samu sakonni daga wurare da yawa, suna tambayar matsayina dangane da halin da ake ciki a jam’iyyar mu ta APC.
Labaran da ake yadawa cewa ina shirin canza sheka zuwa wata jam’iyya ba gaskiya bane. Ni Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano ina nan a cikin jam’iyyar APC, babu wani shiri ko kulli a sarari ko a boye na shiga wata jam’iyya ta daban.
Ya kamata jama’a su sani jam’iyyar APC dani aka yanke mata cibiya, kuma nayi aiki tukuru domin samun kafuwarta da nasararta. Yadda ake tafiyar da ita ne muke jayayya aka kai, kuma maganar tana gaban kotu. Har yanzu muna sauraren hukuncin karshe na kotun koli.
Ina fatan zaku ci gaba da yi mana addu’a ta alheri da fatan dorewar zaman lafiya a Kano da Najeriya.
-MIS
Sardaunan Kano