Zargi: A shafinta na Facebook, gwamnatin jihar Nassarawa ta wallafa wadansu hotuna biynu da ta ke zargin titin Sisinbaki-Kwarra ne, wanda ke karamar hukumar Wamba. A cewarta, hotunan na nuna yanayin titin kafin a gyara, da yadda ya zama bayan da aka gyara.
Wajen bayyana daya daga cikin titunan da gwamnatin jihar Nasarawa ta gina a daya daga cikin kananan hukumomin jihar, masu kula da shafin Facebook din jihar sun yi amfani da hotunan Brazil a maimakon hotunan ainihin titin da gwamnatin ta gyara
Hotunan Brazil ne aka sanya a shafin facebook din jihar Nasarawa wajen kwatanta gyaran da aka yi a titin Sisinbaki-Kwarra da ke karamar hukumar Waje.
Sannu a hankali soshiyal mediya ya zama wani bangare na rayuwar yau da kullun. Yayin da ake cigaba da tabka mahawar dangane da sahihancin bayanan da ke cika dandalin sadarwar. Kungiyoyi da wadansu fannonin al’ummar na amfani da shi wajen fadada ayyukansu da manufofinsu.
A dalilin haka ne shafin gwamnatin jihar Nassarwa ta wallafa hotunan gyaran titin da ta ke yi a Sisinbaki-Kwarra, karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawan Najeriya.
Shafin na da ma’abota 13,000 kuma yana dauke da dubban hotunan da ke nuna irin nasarorin da gwamna jihar, Injiniya Abdullahi Sule ya yi.
A shekarar 2019 aka zabi gwamnan kuma dan kasuwan a karkashin tutar jam’iyyar APC. Shafin na Facebook na bayyana nasarorin shi tun bayan da ya hau ragamar mulkin jihar.
Irin tsokacin da ke kan shafin na nuna cewa yawancin mutane sun dogara da shafin ne wajen samun bayanan gaskiya dangane da abubuwan da ke faruwa a jihar. Misali, wani mai amfani da shafin ya rubuta wadannan kalaman da ke yabon shafin: “Yana kawo wa jama’a labaran duka abubuwan da gwamnatin ke yi ba tare da an tace wani abu ba, labaran zalla ake kawo wa.”
To amma a zahiri, yaya gaskiyar labaran da ke kan wannan shafin?
Takaddama
Labarin wanda ya nuna hotunan titin kafin a fara aiki da bayan da aka kammala ya ja hankalin jama’a domin mutane sama da 200 sun yi ma’amala da labarin, an raba sau 70. Bugu da kari an sake wallafa hotunan a wasu shafukan na daban irin su tiwita, tare da labarin da aka sanya a shafin Facebook.
Misali, wani mai amfani da shafin Tiwita, mai suna Akashe Abdullahi Ari (@AkasheAri) ya wallafa hoton titin da taken: “Kafin ginawa da bayan gina titin Sissinbaki-Kwarra a Wamba mai tsawon kilometa 15.5. Mun gode gwamna Engr. Abdullahi A Sule.”
To sai dai ba kowa ne a shafin ya gamsu da labarin ba, da yawa sun kalubalanci sahihancin hotunan. Wani mai suna Ibrahim ya nuna rashin gamsuwarsa a yayin da ita ma Joan ta ce “Wannan hoton ba Jihar Nasarawa ba ne. wannan ba gaskiya ba ne.”
Jihar Nasarawa jiha ce a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya kuma tana da iyaka da jihohin Filato da Taraba daga gabas, Kaduna daga arewa, jihohin Kogi da Benue daga Kudu dai kuma Birnin Tarayya Abuja daga yammaci.
Tantance Sahihancin Hoton da ya nuna titin lokacin da aka fara gyarawa
Don tantance hoton da ake zargi wai shi ne hoton titin kafin a gyara, mun yi amfani da manhajan Yandex domin gano mafarin hoton.
Manhajar ta Yandex ta nuna mana cewa an fara amfani da hoton ne a wani rahoton da aka wallafa a 2015 wanda ya bayar da cikakken bayani dangane da titin Camacari wanda ke Lauro de Freitas a kasar Brazil.
Hasali ma jaridar Grand Bahia, daya daga cikin manyan jaridun Brazil ce ta yi rahotanni daban-daban dangane da ginin titin. Bacin haka, labarin ya nuna Mateus Pereira na jaridar Grand Bahia a matsayin wanda ya dauki hoton.
Don haka, hoton da ake zargi wai titin Sisinbaki-Kwarra a karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa ne kafin a fara gyarawa ba gaskiya ba ne.
Tantance sahihancin hoton da ke zargin titin Sisinbaki-Kwarra ne bayan an kammala gyara
Da aga yi amfani da manhajan da ke gano ainihin tushen hotuna, sakamakon da aka samu daga kafofin yada labarai da dama sun nuna cewa lallai titin na Sisinbaki-Kwarra ne a karamar hukumar Wamba da ke jihar Nasarawa.
A wani labarin da aka wallafa a Eggonnews, an yi bayanin yadda gwamban jihar ya kaddamar da titin ranar 22 ga watan Mayun 2021.
Wani rahoton da ya bulla a Afridailynewa shi ma ya yi labarin yadda gwamnan ya kaddamar da titin ranar 22 ga watan Mayun 2021.
Rahotannin wadannan jaridun biyu sun yi amfani da wannan hoton. Bacin haka, daya daga cikin hotunan wanda aka yi amfani da shi a Afridailynews ya nuna gwamnan jihar a kusa da wata alama da ta nuna shirin gudanar da aiki a titin Sisinbaki/Kwarra.
To sai dai duk wadannan bayanan ba su gamasar da DUBAWA ba, shi ya sa ta tura wakili zuwa wurin tunda an ce gani ya kori ji. Binciken da aka yi ya nuna cewa hoton da ya nuna aikin da aka kammala a kan titin gaskiya ne. Mazauna al’ummar wadanda suka ga hotunan da aka yi amfani da su a matsayin yadda titin ya ke kafin a fara aiki sun ce ko daya hoton bai yi kama da muhallinsu ba amma wanda aka gama lallai garin su har ma suka kai wakilin DUBAWA wurin ya shaida da kansa.
John Joel wanda ya zagaya da wakilin DUBAWA shi ma ya ce lallai akwai yaudara a hoton.
“Lallai hoton farko ko kusa bai yi da Sisinbaki/Kwarra ba. Ina nan sadda aka fara aikin kuma ba zan iya tuna wani wuri mai kama da nan ba. Amma wanda ke nuna aikin da aka gama nan ne kuma ma zan iya kai ku wurin da kai na.”
Haka nan kuma wani mai mashin Abdullahi Muhammed ya kai wakilin DUBAWA wurin. Daga nan ne DUBAWA ta tabbatar cewa lallai an gina titin Sisinbaki/Kwarra har ma gwamnan jihar ya kaddamar da a shekarar da ta gabata wato 2021. Sai dai hoton da suka yi amfani da shi wajen nuna yadda titin ya ke kafin gyaran ba shi ne ba.
Duk yunkurin da muka yi na ganawa da wadanda ke kula da shafin Facebook na jihar Nasarawar dan jin ta bakin su ya ci tura. Babu wanda ya amsa sakonnin da muka tura a kan shafin na Facebook da ma adireshin email.
Haka nan kuma mun yi kokarin samun jami’an yada labaran gwamnan biyu ta wayar tarho. Shi ma wannan yunkurin ya ci tura domin babu wanda ya amsa wayar har zuwa lokacin da muka yi wannan labarin.
A Karshe
Yayin da DUBAWA ta gano cewa hoton farko ba titin Sisinka/Kwarra da ke karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa ba ne, hoton da aka sa daga baya wanda ke nuna yadda titin ya ke bayan da aka kammala aikin gaskiya ne. Sai dai saboda kasancewar hoton farkon wanda ke da tushe na daban ya sanya alamar tambaya kan sahihancin labarin
Discussion about this post