Rundunar Hisbah dake jihar Jigawa ta fasa kwalaben giya 1,426 a kananan hukumomin Gumel da Dutse.
Shugaban rundunar Malam Ibrahim Dahiru ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Alhamis a garin Dutse.
Dahiru ya ce rundunar ta kama babban jarka mai cin Lita 25 na giyan Burkutu tare da mutum 15 dake da hannu a siyarwa da shan giyan.
Ya ce rundunar ta yi wannan kame a otel da mashaya dake wurare daban daban a kananan hukumomin.
” A ranar 3 ga Afrilu rundunar ta kama kwalaben giya 177 da babban jarka mai cin lita 25 na giyan Burkutu a karamar hukumar Gumel.
“Rundunar ta yi kamen ne a otel din Awala dake hanyar Gujungu, otel din Sabuwar Sahara dake bayan ginin hedikwatar Gumel sannan da Gidan Mama Mai Burkutu.
“A wadannan wurare rundunar ta kama mutum 14 tare da matar dake siyar da Burkutu.
“A ranar 4 ga Maris rundunar ta kama kwalaben giya 1,249 da wurinda ake saka kwalaben gida da Babu komai a ciki guda 143, mota mai lanban rajista MG 194 XA da mutum daya da rundunar ke zargin shine mai mashayar a kauyen Takur Aduwa dake karamar hukumar Dutse.
Ya ce rundunar ta damka Kamen da ta yi wa rundunar ‘yan sandan jihar domin ci gaba da gudanar da bincike.
Dahiru ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye dokokin da gwamnati ta saka a jihar.
Ya ce gwamnati ta hana Sha da siyar da giya a jihar kuma yana mai tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi ƙasa da gwiwa wajen ganin ta kare mutane daga miyagun aiyukka a jihar.