Shugaban Babbar Kotun Tarayya, Babban Mai Shari’a John Tsoho, ya amshi roƙon da Minista Rotimi Amaechi ya yi masa, inda ya ɓalgaci wani sashe na shari’ar da aka maka shi kotu, ya damƙa ta ga wani alƙalin wata kotun daban.
Tsoho ya yi haka ne bisa roƙon da Amaechi ya yi masa cewa idan aka jira sai ranar da aka kammala shari’ar sannan za a san makomar sashen da Amaechi ɗin ya sa aka ɓalgata aka bai wa wani alƙali, to Najeriya za ta riƙa asarar maƙudan kuɗaɗe a kowace rana.
Asalin Gurungunɗumar Kwangilar Da Ta Jawo Aka Maka Amaechi Kotu:
Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Amaechi ya bayar da kwangilar ayyukan sa na’urori da kuma sa-ido kan jiragen ruwan da ke shiga da fita daga tashoshin ruwan Najeriya a kullum
Sai dai kuma ya bayar da kwangilar ce ga wasu kamfanonin da ba wannan harkar su ke yi ba.
Maimakon Amaechi ta bayar da kwangilar ICTN ga kamfanonin fasahar bin-diddigin ayyuka ta hanyar yin amfani da na’urori, sai ya bayar da ita ga kamfanoni biyu, waɗanda a tarihin su, kamfanoni ne masu aikin shigo da kayan asibiti.
Kamfanonin da aka bai wa kwangilar su biyu ne, MedTech Scientific Limited, sai kuma Rozi International Nig. Ltd.
Ganin cewa Hukumar Tantance Kwangiloli ta Ƙasa (BPP) ba ta amince da kamfanonin da Amaechi ya bai wa kwangilar ba, sai Ƙungiyar Kare Haƙƙi ta CASER ta maka Amaechi Ƙara a kotu, a ranar 13 Ga Disamba, 2021.
A cikin ƙarar da CASER ta haɗa har da kamfanonin biyu da Amaechi ya bai wa kwangila.
Yayin da kotu a ƙarƙashin Mai Shari’a Donatus Okoronkwo ya dakatar da Amaechi daga bayar da kwangilar, saboda ƙarar da CASER ta shigar, a ranar 23 Ga Msris, 2022 kuma sai lauyan CASER ya sake garzayawa kotu, ya rubuta wa Mai Shari’a cewa Minista Amaechi ya karya umarnin kotu na ranar 17 Ga Disamba, 2021.
Mai Shari’a ya caji Minista Amaechi da laifin raina kotu, kuma ya umarci ya bayyana gaban sa, domin ya amsa tuhuma.
Zaramboto Da Karankatsagallin Minista Amaechi A Kotu:
Maimakon Amaechi ya bayyana kotu tare da lauyan sa a ranar 9 Ga watan Mayu, 2022 domin a yanke masa hukunci, sai ya zi azarɓaɓin rubuta wa Shugaban Alƙalan Babbar Kotun Tarayya wasiƙa a ranar 31 Ga Maris, 2022.
A cikin wasiƙar, Amaechi ya shaida wa Babban Mai Shari’a John Tsoho cewa, “jinkirin da ake yi kafin a yanke hukuncin shari’ar dakatar da bayar da kwangilar na janyo wa Gwamnatin Tarayya asarar ɗimbin kuɗaɗe a kowace rana a tashoshin jiragen ƙasar nan.
“Don haka ina so a ɓalgaci wani yankin shari’ar a bai wa alƙalin da zai zauna ya yanke hukunci lokacin hutu, domin a wuce wurin.”
Da Farko John Tsoho Bai Yarda Ba:
Da farko dai John Tsoho bai yarda ba, kamar yadda Hadimin sa Ambrose Unaeze ya rubuta wa lauyan Amaechi wasiƙa, a ranar 7 Ga Afrilu, 2022.
Sai dai kuma ranar 13 Ga Afrilu lauyan Amaechi, Lateef Fagbemi ya sake rubuta wa John Tsoho wasiƙar nanata masa tuni. Daga nan ne Shugaban Alƙalan Babbar Kotun Tarayya ɗin ya canja ra’ayi, inda ya amince ya ɓalgaci wani sashen shari’ar domin a bai wa wani alƙalin da ke zama a lokacin hutun Easter, kamsr yadda Amaechi ya nemi a yi.
Yadda John Tsoho Ya Soke Hukuncin Da Ya Yi Da Kan Sa, Ya Biya Bukatar Amaechi:
Washegari a ranar 14 Ga Afrilu, 2022 sai John Tsoho ya aika wa lauyan na Amaechi da wasiƙar amincewa ya ɓalgaci wani yankin shari’ar a gaggauta yanke hukuncin ta a gaban wata kotun.
A wasiƙar, an rattaba cewa Amaechi bai raina kotu ba, kamar yadda Kotun Tarayya a ƙarƙashin Mai Shari’a Donatus ta bayyana. An riƙa kawo hujjoji da bayanan gamsar da hajjar da aka dogara da ita.
CASER Ta Yi Tir Da Hukuncin Biya Wa Amaechi Buƙatar Sa:
Shugaban ƙungiyar Frank Tietie ya la’anci hukuncin da John Tsoho ya yanke, inda ya ce duk kotun da aka ɓalgaci sashen shari’ar aka kai, ba ta yi adalci ba, za ta biya buƙatar Ameachi ne kawai.
“Ai kawai tunda ya bi son ran Minista Amaechi ya biya masa buƙatar sa, babu yadda za a yi adalci a shari’ar kenan.
“Sannan kuma ta yaya za a cire wani yanki na wata ƙara a kai wata kotu daban a yanke hukunci da gaggawa a can? To ita ainihin ƙarar ta farko, ya za a yanke hukuncin ta alhali an yanke wani ɓangare na ƙarar an maka a wata kotu?” Inji Shugaban CASER.