Jagoran jam’iyyar APC Bola Tinubu kuma ɗan takaran shugaban kasa a APC ya baiwa gwamnatin Kaduna gudunmawar naira miliyan 50 domin ɗawainiyar waɗanda harin ya ritsa da su.
Tinubu ya bayyana wannan kyauta ta sa ne a jawabin sa a garin Kaduna a wajen jawabin da ya yi a fadar gwamnatin jihar.
Ya yi ziyarar jaje ne ga gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da mutanen jihar bisa abinda ya faru.
Ya kuma ƙara da cewa wannan kuɗi ya bada su ne a matsayin gudunmawa ga gwamnatin Kaduna domin kula da waɗanda suka jikkita a harin da kuma domin tallafi ga gwamnatin jihar na ɗawainiya da take yi.
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin makon jiya ƴan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ya taso cike da fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna.
Maharan sun kashe mutum 8, sun jikkata da dama wanda ke kwance yanzu haka a asibitin sojoji na 44. Sannan kuma sun yi garkuwa da matafiya da dama.