Wani rahoto da kamfanin bincike mai zaman kan sa na SBM Intelligence ya fitar a ranar Litinin, ya tabbatar da cewa a Jihar Kaduna aka fi kai wa kadarorin Gwamnatin Tarayya tsakanin 2019 har zuwa 2022.
Rahoton ya binciko cewa mahara da ‘yan bindiga sun kai wa wurare 25 mallakar Gwamnatin Tarayya hari daga 2019 zuwa 2022 a Najeriya.
SBM Intelligence ya ce ‘yan bindiga sun kai wa kadarorin gwamnati hari sau 19 a Arewacin Najeriya, yayin da a Kudancin ƙasar aka kai wa kadarorin gwamnati hari sau 6.
A Arewa ɗin kuma rahoton ya ce an fi kai waɗannan hare-hare a Arewa maso Yamma, inda aka kai har sau takwas, amma bakwai duk a Jihar Kaduna, tsakanin 2019 zuwa 2022.
Yankin Arewa maso Gabas ya zo na biyu a Arewa, inda mahara su ka kai hari kan kadarorin gwamnati har sau bakwai.
Jihar Barno aka fi kai harin a Arewa maso Gabas, domin a can ne aka kai dukkan hare-haren da aka binciko a yankin.
Ba abin mamaki ba ne don jihohin Barno da Kaduna ne aka fi kai hare-haren, idan aka yi la’akari da yadda Boko Haram ke ci gaba da illata Barno, sai kuma yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da ɓarna a jihar Kaduna.
A yankin Arewa maso Gabas dai Boko Haram ne su ka ƙaddamar da yaƙi tun cikin Yuni, 2009, inda suka kashe dubban mutane tare da rasa muhalli da sama da mutum miliyan 3 suka yi, suka koma ‘yan gudun-hijira.
Majalisar Ɗinkin Duniya da kan ta ta ce masu gudun hijirar jihar Barno ne mafi muni a Afrika.
A Arewa maso Yamma kuma ‘yan bindiga ne ke kai hare-haren satar dabbobi, kisa da garkuwa da mutane. Tun su na yi wa gari ko ƙauye takakkiya, har ta kai su na tare hanyar su kwashi matafiya su kwashe fasinjojin cikin mota.
Waɗannan ‘yan bindiga sun kashe dubban mutane kuma sun tarwatsa wasu dubban daga gidajen su.
Tun mahara na karɓar kuɗaɗen diyya daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, har ta kai a wasu na ƙaƙaba wa manoman ƙauyuka kuɗaɗen harajin tilas.
Sai dai kuma rikicin na ci gaba da ƙamari ta inda ‘yan sa-kai ke bi su na ramuwar gayya kan ‘yan bindiga.
Yayin da a Jihar Barno aka fi kai wa tashoshin bada wutar lantarki, a Jihar Kaduna kuma ‘yan bindiga sun fi kai wa jirgin ƙasa hari. Sau biyar kenan ana kai wa jirgin ƙasa hari tsakanin 2019 zuwa 2022 a Jihar Kaduna.
Harin baya-bayan nan shi ne wanda aka kai wa jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, inda aka kashe mutum 9, aka ji wa da dama rauni. Sannan kuma an yi garkuwa da wasu da dama, waɗanda har yau su na hannun masu garkuwa ɗin da suka bayyana cewa su ‘yan ‘Ansaru’ ne.
Sau uku kaɗai aka kai wa kadarorin gwamnati hare-hare a Arewa ta Tsakiya, inda a cikin Satumba 2020 wasu tsageru suka kai wa jirgin ƙasa hari a Bwari, wani gari da ke ƙarƙashin Abuja.
Sai kuma cikin Oktoba 2021 da aka banka wa jirgin ƙasa wuta a Offa, cikin Jihar Kwara.
A cikin watan da shekarar ce kuma aka kai wa jirgin ƙasa hari a Mokwa, cikin Jihar Neja.
A Kudu an kai wa bututun mai hari, an kai wa wata masana’anta hari a Edo, kuma an kai wa jirgin ƙasa hari a Oyigbo, cikin Jihar Ribas.
A Kudu maso Yamma an kai hari a titin jirgin ƙasa a Ogun, sai kuma cikin Maris, 2022 da wasu ɓatagari su ka kai wa matatar Ɗangote hari a Ijebu-Lekki, Legas.