Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya bayyana cewa batun ƙoƙarin shigo da tsarin karɓa-karɓar gwamna tsakanin ƙabilar Tiv da Idoma a jihar, ba zai yiwu a zaɓen 2023 ba.
Ortom ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawar musamman da ya yi da PREMIUM TIMES.
Tun da aka kafa jihar dai ɗan ƙabilar Tiv ke mulki, ɗan ƙabilar Idoma bai taɓa yin gwamna a jihar Benuwai ba.
Ƙabilar Tiv ke da rinjaye na yawan jama’a a jihar, sai ƙabilar Idoma da ke kasancewa na biyu a yawan jama’a.
An zaɓi Gwamna Ortom a ƙarƙashin APC a zaɓen 2015. A yayin tsayar da shi, ya ce idan ya hau kujerar gwamna zai yi ƙoƙarin ganin cewa ɗan ƙabilar Idoma ne zai gaje shi.
Amma kuma a cikin wannan tattaunawar aka yi da shi da wannan jarida, Ortom ya ce a zaɓen 2023 ba zai yiwu PDP ta tsayar da ɗan takara daga ƙabilar Idoma ba, saboda dalilai na siyasa.
Da ya ke zayyana dalilan sa ga wannan jarida, Ortom wanda aka zaɓa a ƙarƙashin APC, amma da yau mulki ya yi tsallen-Baɗake ya koma PDP, ya ce bai wa ɗan ƙabilar Idoma takara zai sa APC ta yi amfani da dalilin har ta yi wa PDP mummunan kaye a zaɓen gwamnan Jihar Benuwai ne.
Tun cikin 1976 aka ƙirƙiro jihar, amma Idoma ba su taɓa yin mulki a jihar ba.
“Idan mu ‘yan PDP mu ka bai wa Shiyyar Sanatan C takarar gwamnan Benuwai, to jam’iyyar PDP za ta iya yin biyu-babu, idan APC ta bai wa ɗan ƙabilar Tiv takarar gwamna, to kwata-kwata PDP faɗuwa zaɓe za ta yi warwas.”
Ya ce idan dai ba dukkan jam’iyyu ne sun haɗu sun nuna amincewar kowace jam’iyya ta amince za bi tsarin karɓa-karɓa baki ɗaya ba, to bayar da takara ga Yankin Benuwai ta Kudu ba za su samu biyan bukata ba.
“Amma idan suka amince, to fito da gwamna ɗan wannan yanki ya yi takarar gwamna abu ne mai sauƙi.”
Ya ƙara da matsalar rashin haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki na ƙananan hukumomi tara na Shiyyar Benuwai ta Kudu ne babbar matsalar kasa samun gwamna daga cikin ƙabilar Benuwai.
“Tuni na sha ba su shawara cewa ‘yan siyasar yankin, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki, su yarda su zauna teburin shawara, domin a tattauna, kuma a shawo kan matsalar. Kuma Idoma su roƙi alfarma daga ‘yan’uwan su Tiv, domin a ba su damar tsayar da ɗan takara. Amma har yau Idoma sun ma kasa haɗa kan su.” Inji Gwamna Ortom.