Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta bayyana cewa duk wata gwamnati na kashe Naira biliyan 12 wajen ciyar da yaran makarantar firamare a kasar nan.
Kodinatan zuba jari na ma’aikatar Usman Bindir ya sanar da haka a taron kwana biyu da aka yi da masu ruwa da tsaki a ma’aikatar domin kirkiro kudirorin da za su taimaka wajen inganta shirin ciyar da yaran makarantar firamare ta ƙasa (National Home Grown School Feeding Programme, NHGSFP).
Bindir ya ce kudirorin da za a kirkiro zai taimaka wajen ganin shirin ya ci gaba domin inganta lafiya da ilimin yara kanana a kasar nan.
Ya ce a yanzu haka gwamnati na ciyar da daliban firamare guda miliyan 10 sannan nan da ‘yan watanni masu zuwa adadin yawan yaran zai karu zuwa miliyan 12.
“Bisa ga tsarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kan shirin ciyar da daliban makarantar firamare gwamnati na kashe Naira 100 akan abincin kowani dalibi domin ganin an jawo hankalin yara wajen zuwa makaranta a kasar nan.
“Gwamnati ta hada hannu da UNWorld Food Program domin ganin ta cimma burin ta.
Bayan haka jami’in UN World Food Program Kim Do-Hwan ya ce an shirya wannan taro domin ganin yadda za a tsara ingantattun hanyoyin da za su taimaka wajen ganin shirin ya ci gaba.
Do-Hwan ya ce samar da ci gaba a shirin zai taimaka wajen ganin an kawar da yunwa, inganta aiyukkan noma da inganta kiwon lafiyar yara.
Daga nan shugaban kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya Dr Onallo Akpa ya ce shirin NHGSFP shiri ne dake taimakawa wajen inganta lafiya, ilimin Yara da Samar da ci gaban al’umma.
Discussion about this post