Sufeton ‘Yan Sanda Kamaruddeen Bello ya samu kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane, bayan matar sa ta biya naira 700,000 kuɗin fanso shi.
Masu garkuwa sun kama shi ne tare da wasu masallata biyu a wani masallaci, lokacin da su ke Sallar Isha’i a unguwar Soyoye, Abeokuta, Babban Birnin Jihar Oyo a ranar Lahadin makon shekaranjiya.
Wani jami’in ɗan sanda ya shaida wa wakilin mu cewa an kama Bello yayin da matar sa ce tsakiyar jegon haihuwar ɗa namiji da ta yi, kwanaki huɗu kafin kama mijin na ta, wanda Sufeto ne.
“Bayan sun kama su, masu garkuwar sun nemi a biya su naira miliyan 5 kuɗin fansar kowane mutum ɗaya da suka kama.
“A gaskiya ban san abin da sauran su ka biya ba. Na san dai an sako su tun ranar Alhamis. Shi kuwa Kamaruddeen matar sa ta biya kuɗi za su kai naira 700,000.
“Bayan sun kama su a masallaci, sun yi amfani da lambar wayar ɗaya daga cikin waɗanda suka kama ɗin, su ka kira matar sa.
“An yi ƙoƙarin kada masu garkuwar su gane cewa Kamaruddeen Bello ɗan sanda ne, gudun kada su kashe shi.”
Premium Times ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, kuma ya tabbatar da kamun da aka yi wa abokin aikin na su.
Sai dai kuma ya ce a gaskiya shi dai ban san an biya kuɗin fansa ba.