Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya gargadi tsoffin gwamnonin jam’iyyar da su shiga taitayin su, su dai na ja da gwamnonin jihohin su a jihohin su.
Adamu ya ce a kowacce jiha gwamnan ne shugaban jam’iyya, dole kowa ya yi mubaya’a ya hakura ya bi shi ko yana so ko baya so, idan ko ba haka ba za su saka kafar wando daya da jam’iyyar.
” Abinda ya kamaci tsoffin gwamnonin shine su rika taimakawa da shawarwari domin cigaban jam’iyyar a jihohin su ba gasa da gwamnan jihar ba.
Adam ya kara da yin kira ga duka ‘ya’yan jam’iyyar da su saka jam’iyyar a gaba da komai yanzu domin samun nasara a zabukan dake tafe.
Bayan haka jam’iyyar ta sanar da kudaden fom din takarar kujeru karkashin jam’iyyar.
Taron APC
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba sani ba sabo a zaben fidda dan takarar shugaban kasa da za a yi a cikin watan gobe.
Jam’iyyar ta ce ba za a yi maslaha ba kowa ya wasa wukar sa kawai a dira filin yanka, wanda ya iya fawa wa kwashi babban rabo, ya cira tutar jam’iyyar a zaben 2023 dake tafe.
Wannan yana kunshe ne cikin matsayar da jam’iyyar ta dauka yayin taron majalisar zartarwarta, a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam`iyyar na kasa da jihohi da gwamnoni da sauran jiga-jiganta na kasa baki daya.
Bayan haka jam’iyyar ta sanar da siyar da fom din takarar kujerun ta kamar haka:
Shugaban Kasa naira miliyan 100. Kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30, fom naira miliyan 70
Gwamna naira miliyan 50
Sanatoci naira miliyan 20.
‘Yan majalisar wakilai naira miliyan 10.
‘Yan majalisar jiha naira miliyan biyu.