Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Amaechi ya yi ƙaurin-suna wajen take dokokin bayar da kwangilar biliyoyin nairori, ta yadda ya ke gabagaɗin bai wa kamfanonin da ba su cancanta ba.
Ƙarma-ƙarmar da Amaechi ya yi ta baya-bayan nan, ita ce wadda ya zaɓi kamfani ɗan tagajan-tagajan, ya ba shi kwangilar samar da na’urorin tsaro a ɓangaren sufurin jiragen ƙasa, tsakanin Abuja zuwa Kaduna ta naira biliyan 3.7.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wasu Dalilai 9 da su ka haddasa jinkirin kwangilar samar da na’urorin hangen bam da ‘yan bindiga daga nesa na naira biliyan 3.7, wadda Amaechi ya bayar a ƙudundune.
Yadda Amaechi Ya Bayar Da Kwangilar Na’urorin Tsaron Jiragen Ƙasa Ga Ɗan-tagajan-tagajan:
Rashin bayar da gamsasshen bayani da hujjojin yadda za a sayo na’urorin da kuma tabbacin kamfanin da zai yi kwangilar, sun haddasa samar da jinkiri da kuma ƙin amincewar Majalisar Zartaswa a kwangilar sayen na’urorin hangen bam da ‘yan bindiga daga nesa, wadda Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya gabatar wa Majalisar Zartaswa kimanin watanni shida kafin ‘yan bindiga su kai mummunan farmaki kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin.
Wata takarda ko wasiƙar sirri da ta faɗo hannun wannan jarida ta nuna yadda Majalisar Zartaswa ta yi fatali da wata kwangila da Amaechi ya nemi bayarwa a ƙudundune.
Amaechi ya nemi Majalisar Zartaswa ta amince da kwangilar sayo na’urorin hange da tantance bam ko ‘yan bindiga daga nesa da aka yi niyya maƙala wa jiragen ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Majalisar Zartaswa ta ƙi amincewa ne saboda waɗansu dalilai da suka haɗa da:
Na farko dai Minista Amaechi ya kasa bayar da hujjar cewa kamfanin da zai bai wa kwangilar zai iya kawo kayayyakin.
Sannan Amaechi bai gamsar da Majalisar Zartaswa cewa kamfanin zai iya aikin maƙala na’urorin idan ya shigo da su ƙasar nan ba.
Dalili na uku, Majalisar Zartaswa ba ta amince da kwangilar ba, saboda aiki ne na maƙudan kuɗaɗe, har naira biliyan 3 da ɗoriya. Amma kamfanin da Amaechi ya yi niyyar bai wa kwangilar kwata-kwata bai taɓa yin irin wannan aikin ba.
Wani dalili kuma shi ne Minista Amaechi ya kasa gabatar wa Majalisar Zartaswa irin wasu ayyukan da kamfanin ya taɓa yi a baya, ballantana a gamsu cewa zai iya yin aikin samar da na’urorin.
Sannan kuma Amaechi bai kawo hujja daga wani wuri mai nuna cewa akwai inda aka yi amfani da irin na’urorin kuma a yanzu haka su na aiki sosai.
Wani dalili kuma shi ne, Majalisar Zartaswa ta gano cewa kamfanin da Amaechi ya bai wa kwangilar ɗan tagajan-tagajan ne, gaba ɗaya abin da ke cikin asusun kamfanin bai wuce naira miliyan 84.9 ba.
Sannan kuma kamfanin bai wuce shekaru uku da kafawa ba. Domin an kafa shi ne cikin 2019, sannan kuma ba shi da wata ƙwarewa ko gogewar yin irin ayyukan da Amaechi ya nemi a ba shi.
Wani dalilin kuma shi ne, Amaechi bai gabatar Da sunayen wasu kamfanonin da su ka nema aka hana su ba, ballantana a auna ta su ƙwarewar ko cancantar da kuma ta ɗan tagajan-tagajan ɗin kamfanin da Amaechi ya nemi bai wa kwangilar ba.
Wani dalilin kuma shi ne Amaechi bai yi wa kwangilar dalla-dalla ba. Kamata ya nuna cewa za a kashe kuɗaɗen a jirgin ƙasa masu zuwa garuruwa kaza da kaza. Shin iyakar masu zirga-zirga Abuja da Kaduna ne, ko kuwa har da na sauran garuruwa za a kashe wa kuɗaɗen? Duk Minista Amaechi bai yi haka ba.
Idan ba a manta ba, bayan kai hari kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, Amaechi ya bayyana cewa “da tun tuni an maƙala wa jiragen da ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna na’urorin, to da hakan bai faru ba.”
Sai dai kuma Amaechi bai wa duniya cewa shi ne ya haddasa sakacin ba, saboda ya bayar da kwangilar aikin samar da na’urorin a ƙudundune, kuma ga kamfanin da bai cancanta ba.
“An tsaya ana jayayya akan aikin samar da na’urorin na jiragen ‘drone’ kyamara mai-gani-har-hanji’. Ana buƙatar waɗannan na’urori domin ko daga nesa jirgi ya ke, za su nuna masa akwai matsala daidai wuri kaza da kaza. Idan wasu mutane ne ɗauke da makamai, duk na’urorin za su sanar.” Inji Amaechi.
Amma wasiƙar ƙin amincewa da ƙudundunen da Amaechi ya yi, ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, wadda a Taron Majalisar Zartaswa na ranar 24 Ga Satumba, 2021, aka ƙi amincewa da kwangilar naira biliyan 3.7 ɗin da Ministan na Sufuri ya nemi bayarwa a sunƙaƙe.
Batutuwan da aka tattauna a wurin taron waɗanda aka rubuta, sun faɗo hannun wannan jarida. Sun nuna wani kamfani ne mai suna Mogjan Nigeria Limited wanda aka yi wa rajista a ranar 6 Ga Agusta, 2019 Amaechi ya so a bai wa Kwangilar.
Majiyar Fadar Shugaban Ƙasa ta shaida wa jaridar Punch cewa an ƙi amincewa da kwangilar saboda, “mun yi tantama da tababar ƙwarewar kamfanin, wanda bai ma fi shekaru biyu da kafuwa ba.
“Sannan kuma kamfanin bai taɓa yin aikin da ya kai naira biliyan 3.7 a baya ba. Bai kuma taɓa samar da na’urorin a wani wuri an tabbatar da ƙwarewar sa ba.”
A cikin wasiƙar dai an rubuta cewa Amaechi ya shaida wa Majalisar Zartaswa cewa Hukumar Tantance Kwangiloli ta Ƙasa (BPE) ce ta amince da kamfanin.
Tsakanin Tashar Jirgin Ƙasa ta Idu da ke Abuja da Tashar Jirgin Ƙasa ta Rigasa a Kaduna, tazarar kilomita 200 ce. A can ne Amaechi ke so a kashe zunzurutun naira biliyan 3.7.
Shi kan sa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo wanda ya jagoranci Taron Majalisar Zartaswa a ranar, ya umarci Amaechi cewa ya na so ya san yadda na’urorin za su riƙa aiki idan ana amfani da su tukunna.
Shi kuwa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Ibrahim Gambari, ya nemi sanin shin a tsakanin jiragen Abuja da Kaduna kaɗai za a kashe kuɗaɗen ko har da na sauran garuruwa?
A nan ne Amaechi ya ce ai aikin na gwaji ne, idan ya yi sosai a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, to kuma sai a yi a sauran garuruwan da jiragen ƙasa ke zirga-zirga.
Yadda Amaechi Ya Bayar Da Kwangilar Na’urorin Bibiyar Jiragen Ruwa Ga Malaman Tsafta Da Dillalin Gidaje:
Cikin 2021 PREMIUM TIMES HAUSA ta bankaɗo wata ƙarma-ƙarmar bai wa mai tallar kifi fiɗar saniya, wadda Minista Rotimi Amaechi ya yi, inda ya nemi amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ta bayan fage.
A labarin dai an ji yadda Buhari da Amaechi suka gabji kwangilar aikin tashoshin jiragen ruwa, su ka danƙara wa malaman tsafta da dillalan gidaje.
Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi sun karya ka’idoji da dokokin sharuɗɗan bayar da kwangila, inda su ka ɗauki kwangilar maƙudan kuɗaɗe ta aikin da ya shafi killace bayanan tsaro a Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, suka bai wa kamfanonin da kwata-kwata ba aikin su ba ne, hanyar jirgi daban, ta mota daban.
Kamfanin da aka bai wa kwangilar dai bai san komai a harkar ayyukan tashoshin jiragen ruwa ba. Aikin kamfanin kawai shi ne kwangilar kayan ayyukan lafiya.
Zai yi kwangilar tare da wani kamfanin haɗin-guiwa, wanda shi kuma aikin sa shi ne dillanci da gina manyan rukunin gidaje kawai.
Tuni dai Hukumar Tantancewa da Duba Cancantar Kwangila da Cancantar Ɗan Kwangila (BPP), ta ce wannan lamari da ya faru abin kunya ne da zubar da kuma da mutunci. Sannan kuma ta ce kwangilar haramtacciya ce, amma babu yadda hukumar za ta iya yi, tunda Shugaba Buhari ne da kan sa ya karya ƙa’ida, ya sa hannun amincewar a bai wa kamfanonin da ba su dace kuma ba su cancanta ba kwangilar.
Waɗannan bayanai duk PREMIUM TIMES ce ta bankaɗo su, kamar yadda za ku karanta hujjojin da za a bijiro da su a ƙasa.
Wannan katafariya kuma haramtacciyar kwangila ta jefa manyan jami’an gwamnatin Buhari cikin yanayin jifar juna da habaice-habaicen zargi.
Ita kuwa Hukumar BPP wadda aka karya ƙa’idojin da ta shimfiɗa, aka ɗauki kwangilar aka bai wa kamfanonin da ba a tantance ba, tuni ta rubuta takarda ta rashin jin daɗi, wadda a fakaice kawai takardar wadda PREMIUM TIMES ta gani, ta na nuna cewa Buhari da Amaechi sun karya doka da ƙa’ida, inda su ka ɗauki aikin garambawul ɗin keke su ka bai wa wanda ko ɗaure ƙararrawar keken ma bai iya ba.
Binciken PREMIUM TIMES dai ya dogara ne da wasiƙun da su ka riƙa karakaina, waɗanda ke ɗauke da umarnin Shugaban Ƙasa da umarnin Amaechi da kuma irin martanin da Hukumar BPP ta riƙa maidawa, inda ta ke nuna rashin dacewar da aka nuna, inda aka ƙi bin ƙa’ida.
An Karya Dokar Bada Kwangiloli Ta 2007 -BPP:
Hukumar da ke kula da tantance cancantar adadin farashin kwangila da cancantar kamfanin da za a ba kwangilar, wato Bureau for Public Procurement (BPP), ta ce an karya sharuɗɗa da ƙa’idojin da doka ta gindaya a Dokar Bada Kwangiloli ta 2007.
Aikin kwangilar da ake magana an bayar ɗin dai shi ne aikin yin amfani da na’urorin da ke nunawa ko iya gane duk inda wani jirgin ruwa ɗauke da kaya ya ke (ICTN) idan ya shigo Najeriya da kuma wanda zai fita ko ya fita daga Najeriya.
Wannan aiki ne mai samar da maƙudan kuɗaɗen haraji a ƙasa, idan aka yi shi kamar yadda doka ta tanadar. Sannan kuma aiki ne da ya shafi batutuwan tsaron ƙasa.
Wata wasiƙa da Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta aika wa BPP a ranar 26 Ga Agusta, 2021, ta ce a yanzu za a ci gaba da aikin ICTN, wanda gwamnatin baya ta dakatar.
Yadda Amaechi Da Buhari Suka Ba Mai Tallar Kifi Fiɗar Karsana:
A ranar 11 Ga Satumba, 2020, Ameachi ya rubuta wa BPP wasiƙa ta neman iznin yin wata ‘yan tandar neman aikin kwangiloli ga wasu zaɓaɓɓun kamfanoni domin yin aikin ICTN ga manyan jiragen ruwa masu dakon kaya. PREMIUM TIMES ta ga wannan kwafen wasiƙar.
Ganin yadda a gwamnatin baya wannan aiki ya jawo rikicin da har EFCC ta shiga lamarin, sai BPP ta maida wa Amaechi amsa cewa ba ta yarda a ware wasu zaɓaɓɓun kamfanoni a ce za a yi masu tanda ba. Sai dai a yi bai-ɗaya, irin wadda ƙasashen duniya ciki har da Najeriya su ka amince da ita (ICB).
“BPP ba ta yarda ba. Amma ta yarda a yi tanda ɗin a bisa ƙa’idar da doka da ƙasashen duniya su ka amince. Ta haka za a iya samun kamfanoni waɗanda su ka cancanta daga waje, waɗanda za su iya yin aikin da zai biya buƙata.” Inji amsar BPP ga Amaechi, wadda aka aika masa a ranar 22 Ga Oktoba, 2020.
Amma cikin mamaki a ranar 19 Ga Agusta, 2021, sai Amaechi ya aika wa BPP da sanarwa wadda ke ɗauke da amincewa da sa hannun Shugaba Buhari cewa a bayar da kwangilar kai-tsaye ga MedTech Scientific Limited, wani kamfanin hada-hadar magunguna da kayan asibiti.
MedTech Scientific Limited zai yi aikin ne tare da Rozi International Limited, kamfanin dillancin manyan gidaje da ayyukan gine-gine.
PREMIUM TIMES ta gano cewa babu wasu takardun da da Amaechi ya aika wa BPP domin tabbatar da cewa MedTech Scientific Limited da Rozi International Development Limited sun taɓa ko su na da ƙwarewar ayyukan hada-hadar sa-ido kan manyan jiragen ruwan dakon kaya.
Binciken da PREMIUM TIMES ta yi, ya nuna cewa mai tallar kifi ne aka ba aikin fiɗar karsana kawai.
Dama shi Amaechi karya irin wannan ƙa’ida ba a wannan ce farau ba.
Idan ba a manta ba, wannan jarida ta buga labarin yadda Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da wannan kwangila, saboda zargin damaga da harankazamar da Amaechi ya yi.
Ɗirkaniyar Amaechi A Kwangilar Sabunta Titin Jirgin Ƙasa Daga Legas Zuwa Kano:
A nan ma sai da Amaechi ya lalubo wasu kamfanonin cikin gida waɗanda kwata-kwata ba su da ƙwarewa, ya haɗa su da kamfanin CCECC na Chana, lamarin da ya kawo tsaikon aiki.
Haka kuma hannun Amaechi wajen ganin an maida wa kamfanin INTELS aikin tara kuɗaɗen haraji a tashoshin ruwa, ya nuna irin yadda ministan ke yin katsalandan wajen take dokokin bayar da kwangila.
Malam Mai Gabagaɗi: Yadda Amaechi Ya Dakatar Da Hadiza Bala Daga Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa Ba Bisa Ƙa’ida Ba:
Premium Times ta gano cewa ba bisa ƙa’ida Ameachi a matsayin sa na Ministan Sufuri ya dakatar da tsohuwar Shugabar Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hadiza Bala ba.
Bai rubuta mata takardar gargaɗi da ta neman bayani ba, sai dai ya tura mata takardar dakatarwa kawai.
Amma daga baya Premium Times Hausa ta gano yadda kwangilolin biliyoyin nairori su ka haɗa Amaechi da Hadiza Bala ƙaƙudubar rikici.
Ashe dai kwatagwangwamar rikicin kwangilolin biliyoyin nairori ne su ka haɗa dakatacciyar Shugabar Hukumar Tashoshin Ruwa Hadiza Bala rikici ita da ogan ta, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Wasu gangariyar kwafen takardun da PREMIUM TIMES HAUSA ta damƙe a matsayin hujja, sun nuna cewa watanni kaɗan kafin dakatar da Hadiza a makon da ya gabata, ta tafka ƙadabolon rikici ita da Amaechi, kan wata gawurtacciyar kwangila.
Ƙaƙudubar rigima ta harɗe a tsakanin su, har sai da ta kai Ofishin Tantance Hakikanin Farashin Kwangila (BPP), Ministan Shari’a Abubakar Malami da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari duk sun sa baki a rigimar.
Gambari ya aika wa Amaechi da Hadiza da umarni daga Shugaba Muhammadu Buhari, kuma ya nemi shawara daga waje, domin sasanta lamarin.
Hadiza wadda aka dakatar da ita a lokacin, Minista Amaechi ya yi iƙirarin cewa ta kasa cike giɓin naira biliyan 165 da su ka kamata ta zuba asusun Gwamnatin Tarayya, ta maida raddin cewa lissafin da Amaechi ya dogara da shi, lissafi ne amma na dawakan-Rano.
Gurungunɗuma Da Kwatagwangwamar Kwangilar Da Ta Hada Amaechi da Hadiza Bala Zare Wa Juna Idanu:
Dalla-dallar abin da PREMIUM TIMES HAUSA ta gani da idon ta, wato akwai wata narkekiyar kwangila wadda NPA ta rubuta wa Hukumar Tantance Tantagaryar Adadin Kuɗaɗen Kwangila (Bureau of Public Procurement, wato BPP), inda ta nemi a zaɓi kamfani daga cikin wasu kamfanoni 9 da su ka nemi kwangilar aikin yashe gaɓa da gangar bakin mashigar jiragen ruwa a gefen teku a Lagos. Bonny, Warri da Gundumar Excravos.
PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa kuɗaɗen wannan kwangila sun kai naira biliyan 65.
Kwangilar yasar rairayi da dagwalon kwatamin gefen tekun Lagos ta kai naira biliyan 31. Ita kuma kwangilar yasar rairayi da dagwalon kwatami a Tashar Ruwa ta Bonny, ta kai naira biliyan 34.
NPA ta ce ta nemi bin tsarin zaɓen tantance kamfanin da ya dace ya yi aikin, saboda yanayin irin aikin. Sannan kuma kwangilar aikin haɗa-ka da ake yi tsakanin Kamfanin Kula da Yasar Yashi na Lagos, LPCMC da na Bonny, wato BCN, duk wa’adin cikar aikin su ya ƙare cikin Disamba, 2019 da kuma Yuni 2020.
Hukumar Tantance Tantagaryar Adadin Farashin Kudaden Kwangila, BPP ta amince da tsarin da NPA ta ce a bi wajen bayar da kwangilar.
Katsalandan Daga Amaechi:
Amincewar ke da wuya sai Amaechi ya ce bai yarda da tsarin da aka bi ba, kuma nan take ya soke kwangilar, sannan ya ce kamfanin da ke kan kwangilar wadda wa’adin ta ya cika, to a ƙara masa wa’adin shekara ɗaya.
Amaechi ya ce ya yi haka ne bisa shawarar da ya ce BPP da Hukumomin Gwamnati sun bayar, bisa dalili na barɓewar cutar korona.
Ita kuma Hadiza ta rubuta a cikin wani bayani cewa Minista Amaechi ya yi ƙorafin cewa an maida shi saniyar-ware wajen tsara bayar da kwangilar, kuma ya nuna damuwa dangane da zunzurutun kuɗaɗen da aka ware don biyan kwangilolin.
Sannan kuma Hadiza ta ce kamfanonin da Amaechi ya ce a ƙara wa wa’adin shekara ɗaya, sun shafe shekaru 15 su na wannan aiki. Ga shi kuma wa’adin su ya ƙare a Agusta.
Sannan kuma Hadiza ta ce babu wani dalili da Minista Amaechi zai kafa hujja da cutar korona domin dukkan aikin tantance kwangilolin ta saƙon kar-ta-kwana na tsarin aiken ‘courrier’ aka yi shi.
Daga nan sai ta ce idan Amaechi bai gamsu da kwangilar ba, zai iya umartar NPA a ka’idance ta soke kwangilar sannan ta kara wa kamfanonin da wa’adin su ya ƙare shekara ɗaya.
Cikin wata wasiƙa a ranar 2 Ga Yuni, 2020, ana tsakiyar korona, Ma’aikatar Sufuri ta umarci NPA ta janye sanarwar neman kamfanonin da za a bai wa kwangilar aikin yashe rairayin.
Wani Daraktan Kula da Harkokin Shari’a da Batutuwan Kotu na Ma’aikatar Sufuri, mai suna Pius Oteh ne ya sa wa takardar hannu.
Kuma ya umarci NPA ta ƙara wa kamfanonin da ke kan aikin yashe rairayi da dagwalon gefen teku wa’adin shekara ɗaya.
Nan take NPA ta bi umarnin da Ma’aikatar Sufuri ta bayar.
“Mu Ke Da Ikon Soke Kwangila, Ba Ma’aikatar Sufuri Ba” -BPP
Ganin umarnin da Minista Amaechi ya bai wa NPA, sai Hukumar BPP ta rattaba cewa, “akwai fa ayyukan da cutar korona ba za ta hana aiwatar da su ba, kuma BPP din ce ke da iznin soke kwangiloli ba Ma’aikatar Sufuri a karkashin Amaechi ba.”
Discussion about this post