Gwamnan Kogi kuma ɗan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC, Yahaya Bello ya ce ba shi fargabar haɗa kafaɗa da Bola Tinubu, Rotimi Amaechi a kokuwar samun tikitin zama ɗan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Gwamna Bello ya ce akwai matasa sama da miliyan 16 da suka yi katin zaɓe domin kawai su jefa masa kuri’a ne idan zaben 2023 ya zo.
” Ni dai a shirye nake. Matasa da mutanen Najeriya sun amince da ni kuma ni ne za su zaɓa a zaben 2023. Saboda haka ko shakka babu ina da kyakkyawar yaƙinin cewa nine zan lashe zaɓen 2023.
Da aka yi masa tambaya game da ko baya fargabar gamuwarsa da gaggan ƴan siyasa kamar su Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, David Umahi da suka bayyana aniyarsu na yin takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC gwamna Bello ya ce ” Bani shakkar gamuwa da koma waye a fagen gwabzawa. Tinubun ne ko Amaechi, kai koma waye. A shiga fili a buga a gani, duk sai na kada su.
” Ayyukan cigaba da nayi a jihar Kogi sun isa a zaɓe shugaba kasa.
” Lallai na yarda Tinubu da sauransu ne suka dasa tubalin da aka dora ginin kafa jam’iyyar APC, amma kuma kangon gini bai isa ace ya zama gida ba sai an ɗora masa abubuwa da dama, waɗannan abubuwa kuwa sune namu gudunmawar.
Gwamna ya amsa waɗannan tambayoyi ne a wajen taron musayen ra’ayoyi na ƴan jarida da editoci karo na biyu wanda ake shiryawa karkashin gwamna Bello.