Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa ƙudirori shida hannu sun zama doka, ciki har da Cibiyar Horas da ‘Yan Sanda ta Wudil a Jihar Kano, wadda a yanzu doka ta amince ta riga yin kwasa-kwasai na digiri da bayar da horon ƙwararru.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wasu bayanai biyu da ya fitar ƙarshen mako.
Shehu ya ce dokar Cibiyar Horas da Jami’an ‘Yan Sanda ta Wudil na ɗaya daga cikin dokokin shida da Shugaba Buhari ya sa wa hannu a ranar Juma’a.
Dokar Ƙarin Wa’adin Ritayar Malamai Daga Shekaru 60 Zuwa 65:
Wata doka da Buhari ya sa wa hannu ita ce Dokar Ƙarin Shekaru Biyar ga malaman makarantu daga yin ritaya idan sun kai shekaru 60, wadda yanzu aka ƙara masu shekaru 5, ta koma 65 kenan.
Dokar Kula Da Magungunan Dabbobi:
Ita kuma wannan, doka ce wadda ta samo asali daga Dokar Kula Da Dabbobi ta A17, ta shekarar 2004.
An kafa wannan doka ce domin kare lafiyar dabbobi, ganowa da binciken cututtuka da magance ciwace-ciwacen dabbobi.
Dokar ta kuma ƙunshi matakan sa-ido kan magungunan dabbobi, abincin su, da kuma kula da ingancin lafiya da abincin su.
Dokar Cibiyar Horas Da ‘Yan Sanda Ta 2021:
Wannan doka ta samar da hurumin amincewa wannan kwaleji da ke Wudil a Jihar Kano ta fara gudanar da kwasa-kwasai na digiri da kuma bayar da horon ƙwarewa domin Inganta ayyukan ƙwararru a fannoni daban-daban.
Daga yanzu ita wannan Cibiya ko Kwaleji za ta kasance shugaban ta tilas sai ya kai muƙamin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG). Kuma Hukumar Kula da Aikin Ɗan Sanda (PSC) ce ke da alhakin naɗa shi, bayan Sufeto Janar ya miƙa sunan sa a matsayin wanda ya cancanta. Haka dai Sashe na 8 na dokar ya tanadar.
“Babban Hadimin Shugaba Buhari a Fannin Harkokin Majalisar Tarayya, Umar El-Yakubu ya halarci zaman sa wa dokokin hannu tare da Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa.”
Dokar Kafa Hukumar Gyaran Dokokin Najeriya, Ta 2022:
Doka ce mai asali daga Dokar kafa Dokokin Najeriya ta N118, ta shekarar 2004.
A yanzu ta zama Dokar kafa Hukumar Gyaran Dokokin Najeriya ta 2022. Wannan doka za ta riƙa gyara da kuma inganta ayyukan gudanar da doka bisa tsari mafi cancanta da ƙa’ida.
Dokar Cibiyar Kula Da Lafiya Ta Hong, Ta 2022:
Wannan doka ta amince da kafa ‘Federal Medical Centre a Hong, Jihar Adamawa.
Wannan cibiya ko asibiti zai riƙa kasancewa a ƙarƙashin shugabancin Babban Daraktan Litika, wanda Shugaban Ƙasa ne kaɗai ke da iznin naɗa shi, bisa shawarar Ministan Lafiya, kamar yadda Sashe na 9 na dokar ya tanadar.