A ranar Talata ce kamfanonin sayar da lambobin waya suka fara aiki da dokar kulle duk wani layin da ba a yi masa rajistar haɗa shi da Katin Ɗan Ƙasa ba, wato ‘National Identification Number’, wadda ake kira ‘NIN’ a taƙaice.
Sai dai kuma dukkan kamfanonin na MTN, Glo, Airtel da 9mobile sun fara zartas da kullewar a hargitse, domin sun riƙa kulle har da layukan ɗimbin waɗanda sun rigaya sun yi rajistar haɗa lambobin na su da lambar ‘NIN’ ɗin su.
Waɗanda abin ya shafa sun riƙa nuna fushin su a fili da kuma a soshiyal. Su na nuna cewa abin mamaki da haushi da takaici, sun haɗa lambobin wayoyin su da lambar NIN ɗin su, amma duk da haka an kulle masu layukan wayoyin su.
Dokar dai ta umarci kamfanonin sayar da layukan waya su kulle wadda ba a yi wa rajista da NIN ba, ta yadda ba za a iya yin kira da lambar ba, sai dai a kira lambar kawai.
Sai dai an yi uzirin cewa da zarar an yi wa lambar rajista da NIN, za a buɗe ta mai lambar ya iya yin kira.
“Ni fa ban gane wannan jangwangwama ba. Ya za a kulle min layi alhali tun tuni na haɗa layi na da lambar ‘NIN’ ɗi ta? Wa ya yi min haka? Wannan ai rashin iya aiki ne. Ta yaya za a ce sai mun yi wannan gaganiyar banza a ƙasar mu? Haba!” Haka wani mai suna Onyekachi ya rubuta a shafin sa na Tiwita.
Ɗimbin mutane a garuruwa daban-daban sun riƙa bayyana irin halin da suka shiga bayan an kulle masu lambobi, alhali kuma sun haɗa lambobin da lambar su ta NIN.
PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa kamfanin MTN ya riƙa tura saƙo ga layukan da ya kulle, mai ɗauke da cewa:
“Mu na sanar da kai cewa mun bi umarnin hukuma, mun kulle layin ka saboda ba ka yi masa rajistar haɗa shi da lambar Katin Ɗan Ƙasa ta NIN ɗin ka ba. Daga yau ba za ka ƙara yin kira da layin ba, sai dai a kira ka kaɗai. Idan ka na so ka haɗa shi da lambar NIN ɗin ka, ka danna *785#.”
Ranar 4 Ga Afrilu ne wa’adin rufe duk layin wayar da ba a haɗa da lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) ba -Gwamnatin Tarayya.
Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin daga ranar Talata, 4 Ga Afrilu a kulle duk wani layin wayar da mai shi bai haɗa da lambar katin shaidar ɗan ƙasa (NIN) ba.
Wata sanarwar da Kakakin Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) shi da Kakakin Hukumar Rajistar Katin Shaidar Ɗan Ƙasa (NICM) su ka sa wa hannu, ta bayyana cewa “duk layin wayar da aka kulle daga ranar Talata, ba za a buɗe shi ba, har sai an yi masa rajistar haɗa shi da lambar NIN ɗin mai shi tukunna.”
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Ikechukwu Adinde na NIN da Kayode Adegoke na NICM da suka fitar a ranar Litinin, ta ce “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince daga ranar 4 Ga Afrilu, 2022 a kulle duk wani layin wayar da mai shi bai haɗa shi da lambar katin shaidar ɗan Najeriya ba ta NIN. Sai ranar da ya haɗa sannan za a buɗe masa.
“Kuma an haramta wa layin nasa yin kira, har sai ya yi rajistar haɗa layin da lambar sa ta NIN tukunna.”
An dai bada umarnin kulle layukan ne bayan da aka riƙa ɗage ranar kullewar har sau 10, tun bayan fara yin aikin rajistar haɗa layukan waya da lambar NIN a cikin Disamba, 2020.
Tun farko dai an bijiro da tsarin ne domin a daƙile masu garkuwa da mutane su na neman kuɗin fansa.
Hakan ya sa Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Ma’aikatar Sadarwa ta Ƙasa ta bijiro da tsarin, a matsayin dabarar gano ɓatagari, da kuma lambar da su ka yi kira da ita.
Sai dai kuma duk da kusan lambobin waya miliyan 125 ne aka nemi a haɗa su da NIN, har yau mutum miliyan 78 ne kaɗai su ke da kati ko lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN).
Sannan kuma har yau ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane na ci gaba da amfani da layukan waya masu rajista da marasa rajista su na kiran iyalan waɗanda suka kama, ana kai masu kuɗin fansa.